Tashin Hankali Yayin da Direban Jirgin Sama Ya Gano Maciji Na Boye a Kasan Kujerarsa, Ya Sauka Dakyar

Tashin Hankali Yayin da Direban Jirgin Sama Ya Gano Maciji Na Boye a Kasan Kujerarsa, Ya Sauka Dakyar

  • Wani matukin jirgi ya shiga tashin hankali yayin da ya sauke jirgi cikin gaggawa a wani yankin kasar Afrika ta Kudu
  • Wannan ya faru ne sakamakon gano akwai wani maciji da ya buya a kasan kujerarsa a lokacin da ya dauko jirgin
  • Ya zuwa yanzu, an ce ba a ga macijin ba, matukin zai koma bakin aikinsa nan ba da jimawa ba, inji rahoto

Afrika ta Kudu - Matukin jirgin kasar Afrika ta Kudu ya sha yabo bayan shawo kan jirgi da saukar gaggawa bayan gano wani maciji gamsheka a karkashin kujerarsa, BBC ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa, matukin jirgin, Rudolph Erasmus ya yi wannan namijin aikin ne a lokacin da ya dauko fasinjoji hudu daga birnin Cape Town zuwa Arewacin Nelspruit da safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Rashin Tausayi: Matashi A Kano Ya Yi Ajalin Budurwarsa Yar Shekara 22 Mai Juna Biyu Ta Hanyar Shake Wa

Sai dai, saboda matsalar da aka samu, ya yi gaggawar sauka bayan gano cewa yana dauke da maciji a cikin jirgin na fasinja.

Maciji ya makale a kasan kujerar direban jirgin sama
Maciji, daya daga dabbobi masu hadari | Hoto: pxfuel.com
Asali: UGC

A tattaunawarsa da Times Live, direban ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina duba karkashin kujerata, sai kawai na ga macijin na kokarin mayar da kansa karkashin kujerar.”

Meye illar saran maciji gamsheka?

Masana lafiya sun shaida cewa, saran maciji gamsheka na iya kai mutum ga madakata cikin kasa da mintuna 30 matukar ba a samu damar daukar matakin da ya dace ba.

Hukumomin kasar, musamman ministan sufurin jiragen sama na Afrika ta Kudu sun yaba da kokarin wannan matuku bisa jajircewarsa.

Jairdar News24 ta ruwaito ministan yana yabawa Mr. Eramus bisa namijin kokarin saukar da jirgin ba tare da wata matsala ba.

Wani yanayi direban ya shiga?

A cewar Mr. Eramus, ya shiga wani mummunan yanayi mai rikitarwa, inda jikinsa ya mutu wajen fada wa fasinjojinsa dalilin saukar gaggawan da ya yi.

Kara karanta wannan

Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

A kalamansa:

“Fada musu na yi cewa akwai matsala, akwai maciji a cikin jirgin. Ina da yakinin cewa yana karkashin kujera ta don haka za mu sauka cikin gaggawa.”

Wannan ne dalilin da yasa ya yi saukar ta gaggawa a birnin Welkom da ke kasar don duba halin da ake ciki.

Sai dai, ya shaida cewa, injiniyoyin jirgin sun ce basu ga alamar maciji ba bayan kammala bincike, don haka zai koma aiki a yau Laraba.

A makon jiya ne wani jirgi ya fadi a Amurka, ana fargabar wasu adadin mutane sun mutu a hadarin mai daukar hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.