Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Easter Guda Biyu Ga Ma’aikata a Najeriya
- Gwamnatin Buhari ta ba da hutun bukukuwan Easter a wannan watan, minista ya fitar da sanarwa mai daukar hankali
- A cewar ministan, za a yi hutun a ranakun Juma’a da Litinin na wannan watan na Afrilu da ake ciki
- Ministan ya yi kira ga kiristocin Najeriya da su sanya kasar a addu’ar fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali a irin wannan yanayin
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 7 da Litinin 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun Good Friday da Easter Monday.
Wannan na fitowa ne daga bakin ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranar Laraba 5 Afirilu, 2023 a Abuja.
Ministan ya yi kira ga Kiristoci a kasar da su yi riko da akidar sadaukarwa, hadin kai, yafiya, kirki, soyayya da hakuri a lokacin bukukuwan na Easter.
A cewarsa, halayen da ya bayyana a sama sun yi daidai da dabi’un Yesu Almasihu mai tsarki, kamar yadda rahoton The Nation ya bayyana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran minista ga kiristocin Najeriya
A sanarwar da ministan ya fitar ta hannun sakataren dindindin na ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore ya yi kira ga Kiristoci da su yi amfani da lokacin bukukuwan Easter wajen yiwa Najeriya addu’ar kawo karshen rashin tsaro.
Ya kara da cewa, lamarin da ya shafi tsaro aiki ne da a shafi dukkan ‘yan kasa na gari, inda ya kara da cewa, ya kamata ‘yan Najeriya da ma baki su saka kasar addu’a, rahoton Punch.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Najeriya na yin iyakar kokarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin tsanaki ba tare da samun wata matsala ba.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga a yiwa Najeriya a addu’a a Ramadana
A wani labarin, kunji yadda sarkin Musulmi a Najeriya ya bayyana ganin watan Ramadana, inda ya bukaci Musulmai da su dukufa da yiwa kasar addu’a a cikin watan.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da tashe-tashen hankula a bangarori daban-daban.
Ya kuma bayyana cewa, aikin tabbatar da tsaro a Najeriya na kowa ne, don haka akwai bukatar kowa ya dukufa a wannan fannin.
Asali: Legit.ng