'Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 da Ake Zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne a Jihar Neja

'Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 da Ake Zargin Masu Garkuwa da Mutane Ne a Jihar Neja

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kame wasu mutane biyu bisa zarginsu da sace wasu mutane tare da kashe wani basarake
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da neman wasu da ake zargin dasu aka aikata laifin, za a gurfanar dasu a kotu
  • Jihar Neja na daya daga jihohin da ke fama da barnar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewacin Najeriya

Jihar Neja - Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ce, ta kama wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne bisa hannu a kisan Abubakar Yahaya, mai garin Gusasse a karamar hukumar Bosso ta jihar.

Bayan kashe Yahaya, ana zarginsu da sace ‘yarsa tare da karbar kudin fansa N1.5m kafin daga bisani su sake ta.

Wannan lamari an ce ya faru ne a ranar 15 ga watan Maris na wannan shekarar, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

An kame 'yan bindigan da suka kashe hakimi a jihar Neja
Jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, Wasiu Abidoun ya shaidawa manema labarai a birnin Minna cewa, wadanda ake zargin sun kuma kashe wani mutum mai suna Manir a lokacin harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka hallaka mai gari tare da sace diyarsa

A cewarsa, tsagerun sun bindige mai garin Abubakar Yahaya ne tare da yin awon gaba da diyarsa zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Ya kuma kara da cewa, ‘yan bindigan sun sace wani mutum mai suna Hassan Gusasse da ke yankin.

Bayan haka ne rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar kame su bayan dogon bincike a ranar 31 ga watan Maris.

An kame mutum biyu, bayanai sun fara fitowa.

Wadanda aka kamen sun hada da Risku Suleiman mai shekaru 34 da kuma Haruna Umar mai shekaru 20 dukkansu ‘yan kauyen Kupa da ke Garatu a hanyar Bida, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Dan Basaraken Kano

A cewar sanarwar ‘yan sandan:

“A lokacin da ake bincike, Risku ya amsa cewa yana aikata barnar satar shanu tare da mahaifinsa, wani Suleiman Aga’ala wanda aka gurfanar bisa laifin satar shanu a Angwan Maireke a Beji.
“Ya kuma amsa cewa ya hada baki da abokinsa, Umar Awara daga Lokoja, wanda shi ma ya gayyaci wasu mutum takwas daga Zamfara (su ne) Idrisu, Shadai, Yeli, Yusuf da sauran wadanda ake nema da kuma wani Haruna Umar.
“Ya ce gungun na da hannu a kisan mai garin, da kuma karbar kudin fansa N1.5m na ‘yarsa da suka sace a baya-bayan nan, yayin da suka karbi wani adadin kudin kuma kafin sako Alh. Hassan Gusasse.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya bayyana cewa, a yanzu haka ana ci gaba da neman hanyar kamo Umar Awara da sauran wadanda ake zargin don gurfanar dasu.

A wani labarin, an kame wani mutumin da ke tone kaburbura tare da sace kokon kawunan mamatan da aka binne.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.