Bani da Zabin Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi, Atiku Ya Magantu Kan Zaben Kogi Na Nuwamba
- Atiku Abubakar ya yi watsi da jita-jitan yana goyon bayan Dino Melaye game da zaben fidda gwaman PDP a jihar Kogi
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake kokarin yin zaben fidda gwani a jihar gabanin zaben watan Nuwamban bana
- Atiku ya ce dukkan ‘yan takarar sun cancanta, don haka duk wanda aka zaba zai iya rike tutar PDP hannu bibbiyu
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya yi watsi da jita-jitan cewa yana da dan takarar gaban goshi a zaben fidda gwanin gwamnan Kogi da ke tafe.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwar da hadimin Atiku, Paul Ibe ya fitar a ranar Talata 4 Afirilu, 2023 game da zaben da ke tafe cikin watan nan, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Innalillahi: 'Yan bindiga sun harbe shugaban APC a wata jiha, sun hallaka mazauna kauye
Sanarwar ta bayyana cewa, a yi watsi da duk wani batun da ake yadawa cewa Atiku na da shafaffen dan takarar gwamnan da yake goyon baya.

Source: UGC
Sanarwar ta Atiku ta yi watsi da batun cewa, yana goyon bayan Dino Melaye a matsayin dan takarar gwamnan PDP a jihar ta Kogi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dukkan ‘yan takara sun cancanta, inji Atiku
Hakazalika, Atiku ya yi kira ga dukkan ‘yan takarar gwamnan na PDP da su kauracewa ta’allaka kansu dashi a daidai lokacin da suke ci gaba da gangamin tallata kansu.
A cewar wani yankin sanarwar:
“Atiku ya yi imani da cewa dukkan ‘yan takara a zaben sun cancanci aikin daukar tutar jam’iyyar mai girma ta PDP kuma duk wanda aka zaba ya kamata a ba shi 'yancinsu na yin aikinsu na kundin tsarin mulki na zaban gwani ga jam’iyar PDP.”
Idan baku manta ba, Melaye na daga cikin wadanda suka jajirce wajen tabbatar da kafa gwamnatin Atiku a zaben 2023, amma aka samu akasi hakan bai yiwu ba.

Kara karanta wannan
Rikicin siyasa: 'Yan APC da PDP sun kaure da kazamar fada a wata jiha, an harbi wani
APC ta tantance ‘yan takara, uku ne mafi karfi
A wani labarin kuma, kunji yadda jam’iyyar APC a jihar Kogi ta bayyana ‘yan takarar ta 18 a zaben gwamna na watan Nuwamba da ke tafe nan kusa.
A jerin ‘yan takarar, akwai uku da ke kusa da gwamna Yahaya Bello, wadanda ake tunanin daya daga cikinsu ne zai samu tikitin APC.
Ya zuwa yanzu, jam’iyyun siyasa na ci gaba da shirin tunkarar zaben na watan Nuwamba mai zuwa, inda Yahaya Bello zai sauka.
Asali: Legit.ng