Jihohin Nasarawa, Kogi da Sauran Jihohin da Aka Hako Rijiyoyin Mai a Arewacin Najeriya
- Kusan jihohi hudu ne a Arewacin Najeriya da ke kan neman danyen man fetur, kuma an yi nasarar haifar da mai ido
- A baya-bayan nan, NNPCL ta yi nasarar tona rijiyar mai a jihar Nasarawa da aka ce za ta samar da akalla ganga biliyan 1 na mai
- Jihar Kogi ce ta farko a Arewa da ta samu nasarar shiga jerin jihohin da ke samar da mai a Najeriya, don haka za ta fara samun biliyoyin kudi
A ranar 28 ga watan Maris, kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce, ya gano mai a yankin Ebenyi-1 da ke jihar Nasarawa a Arewacin Najeriya.
Sabuwar rijiyar man da aka tona tana cikin karamar hukumar Obi ce a jihar ta Nasarawa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Rijiyar man Nasarawa za ta samar da ganga biliyan 1 na danyen mai
A taron da NNPCL ya yi na tabbatar da samo man, shugaban kasa Muhammad Buhari ya nemi gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule da Mele Kyari shugaban NNPCL da su yi aikin tabbatar da hakar man a madadinsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Buhari, aikin hakar man ya yi daidai da manufar gwamnatinsa na neman man a yankuna Benue, Anambra, Calabar, Sokoto, Bida da Neja Delta, rahoton Premium Times.
A farko, NNPCL ta kuduri yin taron a ranar 21 ga watan Maris, amma aka dage zuwa ranar 28 ga wata saboda zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
A halin da ake ciki, jihar Nasarawa ta shiga jerin jihohin da za a hako man fetur a Arewacin Najeriya, lamarin da ya karawa jihohin Arewa daraja.
Yadda NNPCL ke neman mai a jihar Gombe
A watan Nuwamban 2022, Buhari ya kaddamar da aikin hakar man fetur a jihohin Arewa, musamman jihar Gombe da Arewa maso Gabashin Najeriya.
NNPCL ya sanar da samo mai a rijiyar da aka haka ta Kolmani River II a tsakanin lardin Benue da tsagin Gongola; tsakanin jihohin Gombe da Bauchi.
A jihar Gombe ne aka samu nasarar samun man fetur na farko a Arewa bayan shafe shekaru ana neman hanyar neman mai a yankin.
A cewar NNPCL, wannan hako na mai zai taimaka matuka wajen jan hankalin masu zuba hannun jari, kirkirar ayyukan yi da kuma kara kudaden shiga ga gwamnati.
Jihar Kogi za ta fara shan romon aikin mai
A watan Oktoban bara, jihar Kogi ta tabbatar da karbar kaso 13% na kudaden da ake ba jihohi masu arzikin man fetur a Najeriya.
Jihar dai ita ce ta farko da ta fara karbar wadannan kudaden na romon albarkacin man fetur da ke ba wasu jihohin Kudu.
A Najeriya, yanzu haka an ayyana jihar a jerin jihohin da ke samar da man fetur, kuma za ta ci gaba da karbar 13% na albarkar mai.
Asali: Legit.ng