Malaman Musulunci 3 da Suke Yin Tafsiri Yayin da ‘Ya ‘yansu ke Ja Masu Bakin Kur’ani

Malaman Musulunci 3 da Suke Yin Tafsiri Yayin da ‘Ya ‘yansu ke Ja Masu Bakin Kur’ani

Nigeria - A halin yanzu, ana shirya darusan Tafsirin Al-Kur’ani mai tsarki a manyan masallatan Najeriya kamar yadda aka saba a watan Ramadan.

Shafin karatuttukan Malaman Sunnah ya tattaro jerin wasu manyan malaman Musulunci wadanda suke yin karatun Tafsiri tare da ‘ya ‘yansu.

Shahararrun malaman da ƴaƴansu ke ja musu baki yayin da su kuma suke fassara Al-Kur'ani sun hada da irinsu Sheikh Jamil Muhammad Sadees.

Haka zalika Dr Umar Garba Dokaji yana yin tafsirinsa ne tare da ‘dansa mai suna Abdallah.

Shi ma Farfesa Mansur Isa Yelwa na fassara Al-Kur’ani ne tare da yaronsa, Alaramma Abdurrahim Mansur Yelwa a gefe, yana jawo masa ayoyi.

Malaman Musulunci
Malaman Musulunci wajen tafsiri Hoto:Karatuttukanmalumansunnah
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan malam da halin malam

1. Dr. Jameel Muhammad Sadees da Abdallah Jameel Sadees

Kara karanta wannan

Lafiyarsa lau: Bayan dogon cece-kuce, hoton Tinubu da matarsa ya bayyana a kasar waje

Dr. Jameel Muhammad Sadees yana tafsirin azumi ne a masallacin cibiyar addinin Musulunci na Agga da yake garin Jimeta a Yola, a jihar Adamawa.

Ko da ‘dansa ya kan ja masa baki, amma wanda yake taimaka masa wajen karanto ayoyin Kur’ani a tafsirin azumin bana shi ne Abubakar Abdulkadir.

2. Dr. Umar Dokaji da Abdallah Umar Dokaji

Fitaccen malamin nan, Umar Garba Dokaji yana gudanar da darasin bana ne tarea Masjid Afhad a da ke garin Gombe, ana cewa ‘dansa yake ja masa baki.

Abdallah Umar Dokaji ya bi sahun mahaifinsa wanda masanin Al-Kur’ani da Fikihun addini ne.

3. Farfesa Mansur Yelwa da Abdurrahim Mansur Yelwa

Mansur Yelwa yana gabatar da tafsirinsa ne a babban malamin jami’ar ATBU a garin Bauchi. Mutane daga garuruwan Bauchi da Katsina su kan je majalisinsa.

Abdurrahim Mansur Yelwa wanda mahadaccin Kur’ani ne da yake taya mahaifinsa tafsiri. Matashin mahaddacin ya shiga gasar musabaka har a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng