Gwamna El-Rufai Ya Shirya Kwamitin Mika Mulki Mai Dauke da Mutane 65

Gwamna El-Rufai Ya Shirya Kwamitin Mika Mulki Mai Dauke da Mutane 65

  • Gwamna El-Rufai ya kafa kwamitin mika mulki ga magajinsa, wanda za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa
  • Kwamitin yana kunshe ne da manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna, ciki har da sakataren gidan gwamnati
  • El-Rufai ya sha bayyana kwarin gwiwarsa cewa, Sanata Uba Sani zai daura daga inda ya tsaya bayan zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris

Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya kwamitin mika mulki na 2023; wanda gwamna mai barin gado Nasir El-Rufai zai ba zababben gwamna Sanata Uba Sani.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwar da mai ba gwamnan shawari kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, jaridar Leadership ta ruwaito.

A cewar sanarwar, kwamitin mai mutum 65 zai yi aiki ne don tabbatar da kaddamar da tsarin manufofin ci gaba na gwamna mai zuwa, wanda zai daura daga inda El-Rufai ya tsaya.

Kara karanta wannan

Sirri Ya Fasu: An Gano Sunan Gwamnan Arewa da Wasu Mutum 2 da Tinubu Zai Ba Manyan Muƙamai Na Farko

El-Rufai ya shirya mika mulki ga Uba Sani
Jihar Kaduna a Arewa maso Yamma | Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Wadanda za su jagoranci wannan kwamitin

Adekeye ya kara da cewa, kwamitin zai tsara hanyoyin shigowar sabuwar gwamnatin jihar a ranar 29 ga watan Mayun 2023, rahoton Daily Post.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, sanarwar ta ce, Balarabe Abbas Lawal, sakataren gidan gwamnatin jihar Kaduna ne zai jagoranci lamuran kwamitin.

A 2015, Lawal ne shugaban kwamitin mika mulki na wancan lokacin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hakazalika, a 2019, ya kasance mataimakin shugaban kwamitin wanda El-Rufai ya samar don komawa mulki.

El-Rufai ya shafe shekaru 8 yana mulki, zai mika wa Uba Sani

A bangare guda, Nuhu Isyaku Buzun ne zai rike mukamin sakataren kwamitin, wanda a yanzu haka shi ne sakataren dindindin a Kaduna a fannin mukamai da harkokin siyasa.

Idan baku manta ba, El-Rufai ya yi mulki a Kaduna tun 2015, yanzu zai sauka bayan shafe wa’adi biyu na mulki a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Kafa Kwamitin Mutum 17 A Kano Don Mika Mulki Ga Abba Gida-Gida, Cikakken Jerin Mambobi

Uba Sani zai maka dan takarar gwamnan PDP a kotu saboda wani dalili

A wani labarin, kun ji yadda dan zababben gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa, ba zai hakura ba, zai maka dan takarar gwamnan PDP a kotu.

A cewar Uba Sani, akwai inda PDP ta yi nasarar da ya zarce misali a zaben gwamnan da ya gabata na gwamna.

Duk da haka, inda baku manta ba Uba Sani na APC ne ya lashe zaben, amma ya ce zai tafi kotu neman hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng