Ganduje Ya Naɗa Attahiru Jega Tsohon Shugaban INEC Mukamin Uban Jami'a A Kano
- Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta nada jami'an gudanar da sabuwar Majalisar Jami'ar Ilimi ta Sa'adatu Rimi, mallakin jihar
- Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC zai kasance Uban jami'a yayin da Oba Moshood Aliiwo zai kasance shugaban majalisar gudanarwar jami'ar
- Kwamishinan yada labaran Kano ya ce hakan ya biyo bayan sahalewa makarantar zama jami'a ta 222 kuma ta 61 mallakin jiha da hukumar jami'o'i ta kasa ta yi
Kano - Majalisar zartarwar Jihar Kano ta amince da nada tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Attahiru Jega a matsayin uban jami'a mallakin jihar, jami'ar ilimi ta Sa'adatu Rimi, Kumbotso.
Majalisar ta kuma amince da nadin Oba Dakta Moshood Aliiwo, a matsayin Shugaban Majalisar Kula da Ayyukan Jami’ar, rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Mallam Muhammad Garba, shi ya sanar da nadin bayan kammala taron majalisar zartarwar.
Ya bayyana cewa an amince da nadin bayan hukumar jami'o'i ta kasa ta amince da makarantar a matsayin jami'ar jiha ta 61 kuma ta 222 a jerin jami'o'in Najeriya.
Garba ya ce nadin ya yi la'akari da bangare na lll sashe na 22 na dokar jami'ar ilimi ta Sa'adatu Rimi Kumbotso.
Malam Garba ya bayyana cewa;
"Sashe na 1, 2, da 3 da dokar ta tanada ya ce, 'shugaban makarantar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai nada uban jami' a, shugaban gudanarwa da yan kwamintinsa."
Ya ce nadin shugaban gudanarwa da yan kwamitin gudanarwa zai gudanar da wa'adin shekara hudu, wanda za a iya sabuntawa da wasu shekaru hudun a matsayin wa'adin karshe.
Garba ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da nadin manyan jami'an gudanarwa da shugaba makarantar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
Sauran mambobin majalisar gudanarwa da aka nada
Wanda aka nada sun hada da Farfesa Isa Yahaya Bunkure a matsayin shugaban kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi, Kumbotso, kuma mataimakin shugaban jami'ar ilimi ta Sa'adatu Rimi. Sauran su ne Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo a matsayin mataimakin shugaban kwalejin (bangaren koyarwa), mataimakin shugaba; Dakta Miswaru Bello a matsayin mataimaki (bangaren gudanarwa); Saminu Bello Zubairu a matsayin rajistara; Ibrahim Muhammad Yahaya a matsayin mai kula da bangaren kudi sai Mabruka Abubakar Abba a matsayin shugabar dakin karatu.
Nadin mataimakin shugaba, rajistara, bangaren kudi, da dakin karatu zai kasance tsahon shekara biyar, yayin da mataimakan shugaba bangaren gudanarwa da bangaren koyarwa zai kasance tsahon shekaru biyu kowanne.
Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti mai mutane 17 don mika mulki ga gwamnati mai jiran gado
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Zartarwa na Jihar Kano ta amince da kafa wani kwamitimi na mutane 17 da zai yi aiki don mika gwamnati mai jiran gado ta Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan labarai da ayyukan cikin gida, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan ga yan jarida bayan taron sati-sati da majalisar ta saba yi a gidan gwamnatin Kano.
Asali: Legit.ng