EFCC: Kotu Ta Karbe N725m da Kadara a Hannun Tsohon Shugaban Hukumar NIMASA
- Babban kotun tarayya da ke Ikoyi ta amince da rokon EFCC na rike dukiyar Patrick Akpobolokemi
- Hukumar EFCC ta na zargin Akpobolokemi ya mallaki wani fili yayin da yake rike da kujerar NIMASA
- Alkali ya gamsu da bukatar da Lauyar EFCC ta kawo, ya amince a tsare filin kafin a kammala shari’a
Lagos - Babban kotun tarayya mai zama a garin Legas ya bada dama a soma karbe N725,345,897.77 da wani fili na Dr. Patrick Akpobolokemi a Legas.
The Nation a rahoton da ta fitar a jiya, ta ce za a raba tsohon shugaban na hukumar NIMASA da wadannan dukiya da ake zargin ta sata aka same su.
EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa ta na zargin ta cuwa-cuwa Akpobolokemi ya samu fuloti mai lamba J 37A 218 a Banana Island.
Alkalin kotun tarayyar, Tijjani Ringim ya saurari korafin Lauyoyin Hukumar EFCC, ya kuma yi umarni a some rike dukiyar kafin a kammala yin shari’ar.
A ofis aka samu filin?
Lauyar EFCC ta fadawa Mai shari’a Tijjani Ringim cewa akwai hujjoji da su ke nuna Dr. Akpobolokemi ya mallaki dukiyoyin ne a lokacin da yake ofis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A dalilin haka, Bilkisu Buhari ta roki kotun ta amincewa EFCC ta bada sanarwa a jaridu cewa an karbe kadarorin domin masu son mallaka su fito.
Buhari ta na so nan da kwanaki 14, kotu ta ba gwamnatin tarayya damar karbe filin har abada.
EFCC ta samu yadda ta ke so
Bayan rokon da Lauyar na EFCC ta gabatar, Mai shari’a Ringim ya gamsu da bayanan, yake cewa ya samu gamsassun hujjoji, don haka ya biya mata bukata.
Tashar talabijin Channels ta ce EFCC ta fake ne da sashe na 17 na dokar manyan sata da makamantan laifuffuka na 2006 da sashe na 44(2b) na tsarin mulki.
"Na saurari bayanin Lauya da kuma takardun da ta gabatar tare da hujjoji wajen gamsar da kotu. Na gamsu da korafinsu, na karbi bukatarsu."
- Tijjani Ringim
Goodluck Jonathan ya nada Patrick Akpobolokemi a matsayin shugaban NIMASA a lokacinsa.
An zargi APC NWC da cinye kudin fam
A makon nan aka samu labari cewa Salihu Lukman ya ce NWC tayi fatali da sashe na 13.3A(xiv) da na 13.4(iv), ana kashe kudi babu ka’ida a jam’iyyar APC.
A wani rubutun Lukman, an ji yana cewa NEC ce mai ikon amincewa da kasafin kudin jam’iyya, ya ce a yau NWC da cin kare ba tare da an yi babbaka ba.
Asali: Legit.ng