Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban APC da Mazauna Kauyuka a Wani Yankin Kogi

Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban APC da Mazauna Kauyuka a Wani Yankin Kogi

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kogi ya bayyana cewa, an kashe wasu mutane da yawa a jihar a wani sabon hari
  • Rahoto ya ce, an kashe wani shugaban APC a gundumar Oganienugu, lamarin da ya tada hankali sosai a jihar
  • Ya zuwa yanzu, gwamnan ya ba da hakuri, ya ce gwamnati za ta yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar

Jihar Kogi - An shiga tashin hankali a ranar Lahadi yayin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki mazauna yankin Oganienugu a karamar hukumar Dekina da ke jihar Kogi.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun hallaka mutane da dama a wannan mummunan harin.

An tattaro cewa, ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne da tsakar dare, inda suka fara harbin kan uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ana tsaka da azumi, 'yan bindiga sun farmaki jihar Arewa, sun kashe jama'a

An kashe shugaban APC na gundumawa a jihar Kogi
Gwamna Yahaya Bello na APC na jihar da aka kai hari | Hoto: @GovYahayaBello
Asali: Twitter

An kashe shugaban APC da gundumar Oganienugu

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, a harin ne aka hallaka shugaban jam’iyyar APC na gundumar, Hon. James Adah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake martani ga abin da ya faru, gwamna Alhaji Yahaya Bello ya yi kira ga a zauna lafiya duk da aukuwar wannan mummunan lamarin.

Hakazalika, ya yi Allah-wadai da wannan harin da aka kaiwa al’ummar da ke zaune lafiya ba tare da tashin hankali ba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Bello ya kara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna adawa da yakar masu cin gajiyar ta’addanci a jihar tare da tabbatar da an hukunta su.

Gwamna Yahaya Bello ya mika ta’aziyyarsa

Daga nan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga wadanda aka kashe, musamman ahalin shugaban na APC Adah da sauran wadanda harin ya shafa.

Kara karanta wannan

Ramadana: Hisbah ta fasa kwalaben barasa na N500 a jihar Kano, ta yi wani bayani

Ya bukace su da su yi hakuri tare da daukar dangana a lokacin fitina irin wannan, gwamnati za ta dauki mataki.

Ya kuma shawarci mazauna jiharsa da su kasance masu bin doka da oda tare da ba jami’an tsaron da aka turo hadin kai wajen tabbatar da zaman lafiya.

An sace ‘yan mata biyu a jihar Zamfara

A wani labarin, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka kutsa har cikin gidan kwanan dalibai suka sace ‘yan mata guda biyu.

Rahoto ya ce, an daure mai gadin gidan ne kafin daga bisani aka sace ‘yan matan; Zainab da Maryam.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don gano inda aka boye daliban na jami’ar tarayya da ke Gusau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.