Tinubu Na Cigaba Da Samun Karbuwa, Cuba, Nicaragua, Da D8 Sun Taya Shi Murnar Lashe Zabe

Tinubu Na Cigaba Da Samun Karbuwa, Cuba, Nicaragua, Da D8 Sun Taya Shi Murnar Lashe Zabe

  • Ana cigaba da tura sakon fatan alheri ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu daga sassan duniya daban daban
  • Kasar Cuba da Nicaragua sun bi sahun kasashen duniya wajen taya Tinubu murna yayin da su ke fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Najeriya da kuma kara jaddada alaka tsakanin kasashen
  • Kungiyar D8 ita ma ta aike da sakon fatan alherinta, inda tace za ta yi aiki da gwamnatin Tinubu don kara fito da manufofin kungiyar

Kasashen Nicaragua da Cuba ta bakin shugabannin kasashen sun bi sahun jerin kasashe wajen taya zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, murnar lashe cin shugaban kasa na 25 ga watan Fabarairun 2023.

Hakazalika, kungiyar kasashe maso tasowa, D8, ita ma ta taya zababben shugaban murnar nasarar lashe zaben, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

To fah: INEC ta yi hayar wasu manya, fitattun lauyoyi 9 a Najeriya don kare sakamakon zaben 2023

Bola Tinubu
Zaben Najeriya: Cuba, Nicaragua, D8 Sun Taya Tinubu Murna, Sun Yi Alkawarin Mara Masa Baya. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Shugabannin Kasashen Cuba Da Nicaragua Sun Taya Tinubu Murna

A takardar taya murna ga Tinubu dauke da sa hannun Shugaba Maguel Diaz-Canel Bermudez, gwamnatin Cuba ta bayyana zaben a matsayin abin da ke tabbatar da kara karfafa alakar tarihi mai karfi da ke tsakanin kasashen biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A nata bangaren, Nicaragua ta yi fatan alheri ga Najeriya ta hanyar neman zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kasar.

Takardar da ke dauke da sa hannun Shugaba Daniel Ortega Saavedra da Rosario Murillo ta ce:

"Babban fatanmu shine samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Najeriya, yayin da mu ke cigaba kare zumunci mai karfi da yan uwantakar da ke tsakanin mutane da gwamnatin kasashen"

Muna Fatan Yin Aiki Da Gwamnatin Ka, D8 Ga Tinubu

Sanarwar D8, dauke da sa hannun babban sakatarenta, haifaffen Najeriya Ambasada Isiaka Abdulqadir Imam, ta yabawa Najeriya bisa kasancewarta a kungiyar don bayan kafata sama da shekara 25, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

“Ba Za a Rantsar Da Tinubu Ba:” Magoyin Bayan Peter Obi Ya Fasa Ihu a Bidiyo, Ya Hana Jirgin Sama Tashi

Ta ce:

"Najeriya ta kasance babban cikin kungiyar D8. Kasar ta dauki nauyin shirin kungiyar na tallafin lafiya (D-8 HSP) a Abuja kuma ta na shirin daukar nauyin koyar da sana'o'i. Najeriya kuma shirin daukar nauyin shirin kungiyar D8 na farko a fannin makamashi a Lagos nan da tsakiyar 2023."

Da ya ke magana akan gwarin gwiwar da su ke da shi kan Najeriya karkashin gwamnatin Tinubu shi ne za a samu karuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a matsayinta na cibiyar tattalin arziki a Afirka da duniya, D8 ta kara da cewa:

"muna fatan yin aiki da gwamnatinka don fito da ayyuka da kudirorin kungiyarmu."

Ganduje ya kafa kwamitin mika mulki ga zababben gwamna Abba Kabir Yusuf

A wani rahoto, kun ji cewa Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano mai barin gado ya kafa kwamiti na mutane 17 don mika mulki ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zababben gwamna.

Kara karanta wannan

Peter Obi, Datti: Tinubu Ya Rubuta Wa NBC Takarda, Yana Son A Hukunta Channels TV, Ya Bada Dalili

An amince da kafa kwamitin ne a taron majalisar zartarwa ta Kano da aka yi a gidan gwamnatin Kano a cewar kwamishinan yada labarai na Kano, Malam Muhammad Garba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164