'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Dakin Kwanan Dalibai Mata a Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da 2
- Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu ‘yan mata daliban jami’ar tarayya da ke Gusau
- An ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun kutsa har cikin dakin kwanan dalibai, inda suka yi awon gaba dasu
- Ya zuwa yanzu, jami’ai na ci gaba da aiki don tabbatar da sun ceto ‘yan matan da kuma kame ‘yan ta’addan
Bungudu, jihar Zamfara - Wasu tsagerun ‘yan bundiga sun sace dalibai mata biyu na jami’ar tarayya da ke Gusau (FUGUS) a jihar Zamfara.
An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi 2 Afirilu, 2023 lokacin da ‘yan ta’addan suka farmaki dakin kwanan daliban da ke Sabon-Gida.
Sabon-Gida dai wani kauye ne da ke kusa da babban kofar jami’ar, kuma ‘yan ta’addan sun daure masu gadin gidan daliban ne kafin aikata barnar satar.
Rahotanni sun ce, ‘yan matan da aka sacen sun hada da wata mai suna Maryam da kuma Zainab, rahoton Channels Tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana yadda ya faru.
A cewarsa, ‘yan ta’addan sun mamaye dakin kwanan daliban ne da ke kauyen Sabon-gida a karamar hukumar Bungudu da ke jihar ta Arewa maso Yamma, Daily Trust ta ruwaito.
A lokacin da suke barnar, an ce sun daure masu gadin gidan daliban, inda suka kwace wayoyinsu kafin tafiya da daliban da ke karatu a tsangayar kananan kwayoyin halittu (Microbiology).
Bayani daga ‘yan sanda da kuma kokarin da suke yi
A cewar kakakin:
“A lokacin da muka samu rahoto, rundunar ‘yan sanda ta gaggauta zuwa wurin, amma aka tara har ‘yan ta’addan sun tsere da wadanda suka sacen zuwa wani wuri.
“Kwanishinan ‘yan sanda daga baya ya tura jami’ai domin aikin ceto wadanda aka sacen cikin koshin lafiya, tare da kamo wadanda suka yi barnar da kuma gurfanar dasu a gaban kotu.”
Kakakin ya kara da cewa, kwamishina Kolo Yusuf ya bukaci mazauna da su kwantar da hankali tare da ba ‘yan sanda hadin kai a kokarinsu na ceto ‘yan matan cikin koshin lafiya.
‘Yan ta’adda sun hallaka mutane 5 a Katsina
A wani labarin kuma, kunji yadda ‘yan ta’adda suka hallaka mutane biyar a sabon harin da suka kai wani yankin jihar Zamfara.
Wannan lamari ya zo da tashin hankali, kasancewar wannan ne karon farko da ‘yan bindigan ke yin kisa a yankin.
Majiya ta bayyana yadda lamarin ya faru da kuma yadda ‘yan ta’addan suka yaudari mazauna kamar mutanen kirki.
Asali: Legit.ng