Sojoji Sun Sheke Yan Ta'adda Guda 11 A Birnin Gwari, Kaduna

Sojoji Sun Sheke Yan Ta'adda Guda 11 A Birnin Gwari, Kaduna

  • Jami'an sojin Najeriya sun yi nasarar kashe 11 daga cikin yan bindiga a musayar wuta a karamar hukumar Birnin Gwari
  • Jami'an sun kuma lalata sansanonin yan bindigar da dama tare da kwato makamai da lalata baburan hawa
  • Gwamnatin Kaduna ta yaba da kokarin sojoji tare da horarsu da su cigaba da kokari don tabbatar da nasarar kawo karshen yan bindiga

Kaduna - A cigaba da yakar yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma, jami'an rundunar sojin Najeriya sun kashe yan bindiga 11 lokacin musayar wuta a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna, ta ce jami'an sun shiga wurare da dama, tare da tarwatsa sansanin yan bindiga a Bagoma, Rema, Bugai, Dagara, Sabon Layi, Gagumi, Kakangi, Kataki da Randagi.

Gwamna El-Rufai
Sojoji Sun Sheke Yan Ta'adda Guda 11 A Birnin Gwari, Kaduna. Hoto: Gwamnatin Kaduna
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta, Sun Kashe Mutane Akalla 15 Ana Tsaka da Sallah a Masallaci

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi da kwamishinan harkorkin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan, ya ce, a lokacin atisayen, jami'an sun yi arangama da yan bindiga a Kakangi da Kataki, kuma yayin musayar wuta, yan jami'an sun yi galaba kan yan ta'addan bayan sun sha ruwan wuta.

Ya ce an kashe 11 daga ciki yayin da sauran suka tsira da munanan raunika.

Lokacin atisayen, jami'an sun kwato bindiga biyu kirar AK-47, harsashi 57 da kuma lalata babura shida mallakar yan bindigar kamar yadda Zagazola shima ya rahoto.

A daya bangaren, Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana gamsuwa kan atisayen, da kuma yabawa babban kwamanda da ke jagorantar atisayen, Manjo Janar Taoreed Lagbaja bisa jagorancinsa.

Gwamnan ya kuma yaba da kokarin jami'an da nunawa, ya kuma roki su cigaba da haka don cimma nasara.

Yan Sanda Sun Kama Wani Barawo A Abuja, An Kwato Motocci Da Wasu Kayayyaki A Hannunsa

Kara karanta wannan

Manyan Arewa Sun Fusata, Sun Aike da Muhimmin Sako Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

A wani rahoton, yan sanda na jihar Nasarawa sun tabbatar da kama wani mutum da aka dade ana sa ido kansa saboda zargin sata a karamar hukumar Karu, a Abuja.

DSP Rahman Nansel, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa an dade ana sa ido a kansa.

Nansel ya ce an kama shi ne a birnin tarayya Abuja, an kuma kwato motocci biyu daga hannunsa da talabijin da tukunyar gas da ipad da wayoyin salula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164