Shugaban Jam’iyyar NNPP Ta Su Kwankwaso Ya Hakura, Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Shugaban Jam’iyyar NNPP Ta Su Kwankwaso Ya Hakura, Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

  • Shugaban jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso ya bayyana yin murabus daga kujerarsa ta shugabancin jam’iyyar
  • Shugaban ya bayyana dalilinsa na ajiye aiki a daidai lokacin da jam’iyyar ke ci gaba da jimamin rasa zaben shugaban kasa na bana
  • A bangare guda, Kwankwaso ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyar bata yi nasara ba a zaben shugaban kasan da ya gabata

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, farfesa Rufai Ahmed Alkali ya yi murabus daga mukaminsa, jaridar Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar NNPP da dan takararta na shugaban kasa ne suka zo na hudu a zaben shugaban kasa na bana da aka yi a watan Faburairu.

A bangare guda, jam’iyyar ta yi nasarar kafa gwamnati a jihar Kano, inda dan takararta Abba Kabir Yusuf ya lashe zaben gwamna.

Kara karanta wannan

Daga karshe, Kwankwaso ya fadi dalilin yasa bai ci zaben 2023 ba, akwai laifin INEC

Alkali ya ajiye mukaminsa na shugaban NNPP na kasa
Farfesa Rufai Ahmed Alkali | Hoto: nigerianpilot.news
Asali: UGC

Tuni hukumar zabe mai zaman kanta ta ba Abba takardar shaidan lashe zabe, inda ya bayyana shirinsa ga Kanawa kafin ma ya kama aikinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda Alkali ya ajiye aikinsa a NNPP

A wasikar da ya rubutawa sakatarern jam’iyyar a ranar 31 ga watan Maris, Alkali ya ce ya ajiye mukaminsa ne domin share fagen yin gyara da garanbawul ga jam’iyyar da kuma shirinta a nan gaba.

Wasikar tasa na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da gamayyar kwamitin shugabanninta na kasa suka yi wata ganawa mai muhimmanci.

A bangaren ajiye aikin, wasikar ta nuna Alkali na tura ta ne ga jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Kwankwaso da shugaban kwamitin amintattu Cif Boniface Aniebonam.

Hakazalika, wasikar tana nuni da zuwa ga sakataren kwamitin amintattunta na kasa, Injiniya Buba Galadima, rahoton The Nation.

Dalilin da yasa bamu yi nasara a zaben shugaban kasa ba, bayanin Kwankwaso

Kara karanta wannan

Duk Da NNPP Ta Yi Nasara A Kano Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya magantu kan dalilin faduwarsa a zaben shugaban kasa da ya gabata a kasar ranar 25 ga watan Faburairu.

Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, laifin INEC na rashin buga takardun zaben shugaban kasa yadda za a ga tambarin NNPP rangadadau a lokacin da ake kada kuri’u a kasar.

Ya ce, ba zai tafi kotu ba, amma a ka’ida ya kamata ya tafi kotu domin tabbatar da soke zaben da aka yi a kasar gaba dayansa don bin kadun jam’iyyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.