INEC Ta Ware Manyan Lauyoyi 9, Da Biliyoyin Kudade Domin Kare Sakamakon Zaben 2023

INEC Ta Ware Manyan Lauyoyi 9, Da Biliyoyin Kudade Domin Kare Sakamakon Zaben 2023

  • Hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa, ta ware manyan lauyoyi tara da za su kare ta a gaban kotu a Najeriya
  • Lauyoyin za su yi aiki ne don tabbatar da ingancin sakamakon zaben da hukumar ta INEC ta sanar a watan jiya
  • ‘Yan takara a jam’iyyu daban-daban sun ce basu amince da sakamakon zaben da aka yi ba a Najeriya saboda dalilai

FCT, Abuja - Akalla manyan lauyoyin Najeriya tara ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta nada domin kare sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu a gaban kotu.

A cewar City Lawyer, babban lauya kuma tsohon shugaban NBA, Abubakar Mahmud (SAN) ne zai jagoranci tawagar wadannan kwararru.

Sauran jiga-jigan lauyoyin sun hada da Stephen Adehi (SAN), Oluwakemi Pinheiro (SAN), Miannaya Essien (SAN), da Abdullahi Aliyu (SAN).

Kara karanta wannan

Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni

INEC ta yi hayar manyan lauyoyi don kare nasarar Tinubu
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Mahmud Yakubu | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Punch ta tattaro cewa, akwai manyan lauyoyi hudu da ke aiki a sashen shari’a na INEC da za su yi aiki a shari’ar, cikinsu har da Gaba Hssan, Musa Attah da Patricia Obi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC ta ware kudade don kare kanta

Hakazalika, INEC ta ware kudaden da suka kai N3bn domin kare sakamakon zaben shugaban kasan da na ‘yan majalisu har ma da na gwamnoni da aka yi a kasar.

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta ruwaito a baya yadda ‘yan siyasan da suka fadi a zaben bana suka bayyana tafiya kotu don kalubalantar sakamakon zaben.

Ya zuwa yanzu, an shigar da kararrakin kalubalantar zaben akalla guda 100 daga jam’iyyu daban-daban na kasar, Within Nigeria ta tattaro.

Wasu ‘yan takarar shugaban kasa basu amince da sakamakon zaben ba

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, na Labour Peter Obi, na AA Solomon Okangbuan da na APM Chidi Ojei duk sun ce basu amince da sakamakon zaben ba.

Kara karanta wannan

INEC Ki Sake Zaben Gwamna Na Jihar Kaduna – Masu Saka Ido

Idan baku manta ba, a ranar 1 ga watan Maris ne hukumar zabe ta INEC ta sanar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu.

Dalilin da yasa na fadi zabe, Kwankwaso ya magantu

A gefe guda, dan takarar shugaban kasa a NNPP, Rabiu Musa Knwakwaso ya bayyana dalilin da yasa bai ci zaben bana ba.

Kwankwaso ya ce, hukumar zabe ta INEC bata buga takardun zaben yadda jama’a a za su ga tambarin NNPP da kyau ba.

Ya zuwa yanzu, Kwankwaso bai bayyana tafiya kotu kalubalantar zaben ba kamar yadda sauran ‘yan siyasa suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.