Dalilin da Yasa Jam’iyyar NNPP Ba Ta Taka Rawar Gani Ba a Babban Zaben 2023, Bayanin Kwankwaso
- Dan takarar shugaban kasa na NNPP ya bayyana dalilin da yasa jam’iyyarsa bata ci nasara a wasu jihohin kasar ba
- A cewarsa, an samu kuskuren bugun takardun zabe, wanda ya hana jama’a ganin tambarin NNPP da kyau
- Shugaban NNPP na kasa, Farfesa Alkali ya ba wadanda suka lashe zabe a jam’iyyar shawarin yin aiki tukuru
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, jam’iyyarsa bata yi nasara a jihohi da yawa bane saboda tambarin jam’iyyar bai fita da kyau ga masu kada kuri’u ba.
Kwankwaso ya bayyana cewa, munin bugun takardun zabe ne ya sanya mutane rashin ganin tambarin jam’iyyar, The Nation ta ruwaito.
A cewarsa, wannan dalilin ya kai jam’iyyar ta nemi soke zaben da aka yi a kasar gaba dayansa saboda ba a yi mata adalci ba.
Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci hukumar zabe ta INEC da ta gyara wannan kuskuren a zabuka masu zuwa a kasar a nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai lauje cikin nadi
A bangare guda, shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Rufai Ahmed Alkali ya bayyana cewa, duba da nasarar NNPP, zai zama somin tabi ne ga wasu jihohin da za su biyo baya.
A cewarsa, zaben shugaban kasa na 2023 ya bar baya da kura; fushin jama’a, bacin rai da rashin tabbas har ma da dasa alamomin tambayoyin da basu da amsa, rahoton Daily Sun.
Ga wadanda suka lashe zabe a karkashin jam’iyyar, Alkali ya shawarce su da su cirewa jam’iyyar kitse a wuta ta hanyar yin ayyukan kirki kuma alheri don gaba.
Musamman a jihar Kano, ya shawarci Abba Kabir Yusuf da ya bi tafarkin Kwankwaso domin yiwa Kanawa ayyuka masu ma’ana da za su amfani talaka.
Ba zan tsoma baki a mulkin Kano ba, inji Kwankwaso
A wani labarin, kun ji yadda Kwankwaso yace ba zai shiga harkar tafiyar da mulkin sabon gwamnan jihar Kano ba, Abba Kabir Yusuf.
Kwankwaso ya fadi hakan ne a matsayin martani ga wadanda ke tunanin tsohon gwamnan zai ke katsa-landan cikin mulkin jihar ta Kano da ke Arewa maso Yamma.
A cewar Kwankwaso, idan Abba Gida-Gida ya tafka kuskure a mulkinsa zai tabbatar da jawo hankalinsa tare da daura shi kan turba.
Asali: Legit.ng