'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kauyen Katsina, Sun Hallaka Mutane 5 Nan Take
- ‘Yan ta’adda a jihar Katsina sun hallaka mutane biyar tare da jikkata wasu hudu a wani kazamin hari
- Wannan ne karon farko da aka taba kashe mutane a yankin da lamarin ya faru, inji wata majiyar yankin
- Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta fadi gaskiyar abin da ya zo gabanta game da harin
Funtua, jihar Katsina - Wasu ‘yan bindinga sun hallaka mutane biyar tare da raunata wasu hudu a unguwar Barebari da ke gundumar Dukke a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin, wanda ya ce an kashe ‘yan uwansa a harin ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 8:30 na dare.
A cewarsa, sun yi shiga ne kamar na mutanen kirki, inda suka shiga jama’a tare da aikata mummunan aikin.
Sun shigo kamar mutanen kirki
Ya kuma shaida cewa, a lokacin da suka shigo kauyen, sun rarraba kansu ne a zagayen garin don samun damar aikata barnar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa:
“Daga nan ne suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da razana mazauna.
“Akwai wani wuri da muke kira Gidan Ruwa, inda mutanenmu ke buya duk lokacin da aka kawo hari.
"Sai dai, a wannan karon ‘yan ta’addan sun toshe wurin tare da kiran mutane kamar mutanen kirki. A nan aka kashe dan uwana."
Yadda aka kashe ‘yan uwansa
Ya kuma bayyana ‘yan ta’addan suka kashe sauran mutanen a wurare daban-daban tare lalata abubuwa da yawa.
A cewar wani mazaunin yankin na daban, ‘yan ta’addan sun jikkata mutane hudu, inda suka samu raunukan harbin bindiga a harin.
A cewarsa, wannan ne karon farko da aka kai hari irin wannan da aka kashe mutane a kauyen, inda yace galibi ana sace mutanen yankin ne tare da neman fansa.
‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
An tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Gambo Isa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai, ya ce rahoton da ‘yan sanda suka samu na farko ya yi bayani na yadda aka harbi wani ya samu rauni, amma ya mutu a asibiti.
A bangare guda, ‘yan ta’adda sun sha kashi a hannun ‘yan sandan jihar Abia, inda aka sheke ‘yan IPOB biyar.
Asali: Legit.ng