Yan Ta'adda da Dama Sun Mutu Yayin da Suka Kaiwa Yan Sanda Hari a Abia
- Jami'an rundunar yan sanda sun yi nasarar daƙile harin yan ta'addan IPOB a jihar Abiya
- Kwamishinan 'yan sanda ya ce mambobin IPOB/ESN sun yi yukurin kai wa jami'ai hari amma suka kwashi kashinsu a hannu
- Wasu mazauna sun ce mambobin ƙungiyar na gudanar da zanga-zangar lumana a Aba lokacin da abun ya faru
Abia - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Abiya ta ce ta yi nasarar daƙile mummunan harin da mambobin ƙungiyar 'yan aware suka yi yunkurin kaiwa jami'anta.
Punch ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, Geoffrey Ogbonna,ya fitar a madadin kwamishinan 'yan sandan Abia, Mustapha Bala.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa yan sanda sun harbe mambobin IPOB 5 har lahira a Osusu Aba yayin da suka mamaye yankin Aba.
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankin sun yi ikirarin cewa ƙungiyar ta yi zanga-zangar lumana cikin kwanciyar hankali ba tare da ta da zaune tsaye ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani ganau, Chinomso Aka, ya ce mambobin IPOB na tsaka da zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare shugabansu, Nnamdi Kanu, ranar Jumu'a lokacin da lamarin ya auku.
Menene gaskiyar abinda ya faru?
Amma a sanaewan da rundunar yan sanda ta fitar, kwamishina ya ce:
"Ranar 31 ga watan Maris, 2023, wasu mambobin IPOB/ESN suka farmaki dakarun 'yan sanda a cikin birnin Aba. Jami'ai sun yi nasarar daƙile harin ba tare da rasa rayuka da yawa ba."
"Yan ta'addan sun zo da muggan makamai kamar Bam ɗin Fetur, Adduna da Wuƙaƙe da sauransu, bisa tilas maharan suka ari na kare domin tsira da rayuwarsu."
Daga nan rundunar yan sanda ta gargaɗi duk wani mutumi ko ƙungiyar da ke nufin gurbata zaman lafiya a jihar Abiya ya sake tunani tun da wuri.
Rundunar soji ta rasa dakaru 4
A wani labarin kuma Sojojin Najeriya Hudu Sun Kwanta Dama a Wani Mummunan Hatsari a Bauchi
Kwamandan FRSC mai kula da shiyyar Bauchi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sauran mutane 13 da haɗarin ya shafa na kwance a Asibiti.
Asali: Legit.ng