Wasu Yan Uwa Mata 6 A Gombe Sun Maka Basarake A Kotu Kan Gonar Gado
- Wasu mata shida yan uwa sun shigar da karar dagaci bisa zargin cinye musu gonar gado
- Masu karar sun bukaci kotun da ta karbe gonakin tare da dakatar da duk wani abu a cikin gonar gadon na su
- Bangaren wanda ake kara sun bukaci a ba su lokaci don nazarin tuhumar da aka gabatar kafin su mayar da martani
Gombe - Alkalin babbar kotun Gombe, Daurabo Sikkam, ya amince da bukatar wanda aka yi kara a wata shari'a da wasu yan uwa mata shida suka shigar da wani dagaci, Zubairu Ahmadu da wasu mutane uku.
Yan uwan sun hada da Aliona Toddo, Ronny Toddo, Hassana Toddo, Hussaina Toddo kamar yadda The Punch ta rahoto.
Wakilin majiyarmu ya ruwaito cewa wata kungiya mai zaman kanta ce 'Global Pan Africanism Network' ta shigar karar Ahmadu, bisa zargin kwace wa yayan Toddo gonar da suka gada daga mahaifinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An zargi basaraken da hada kai da Julius Lamido, Jude Maigari, da Dolton Toddo, don kwace filin saboda kansancewar su mata.
Da ya ke magana, lauyan GPAN shiyyar Arewa maso Gabas, Barista Ibrahim Ambore-Nuhu, wanda ya tsayawa ma su kara a zaman kotun na farko ranar Alhamis, ya shaidawa yan jarida cewa karar su na rokon kotun ta tabbatar da ma su kara a matsayin mammalakan gonar da ke Ladongor, Lakwantangalan da Lakaikai da kuma gida da ke Kalmai, Billiri, a Jihar Gombe.
Kotu ta hana siyar da gonar
Sun kuma bukaci kotun da ta hana siyar duk wani sashe na gonar magadan da ke Ladongor, Kalmai Billiri Jihar Gombe, inda wanda ake kara na hudu ya siyarwa wanda ake kara na hudu, na biyu da na uku ba tare da izinin masu karar ba.
'Matsalolin' Najeriya Na Hana Ni Barci, Har Na Kamu Da Rashin Lafiya, Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman
Ya ce:
"Bisa ga dokar kasa da sashi na 42 na kundin mulkin 1999, ma su karar ne ke da hakkin mallakar kadarorin mahaifinsu (Amin Toddo).
"Mu na rokon kotu mai alfarma cewa gonaki da ke Ladongor, Lakwantangalan, Lakaikai da kuma gidaje da duk wata kadara da marigayi mahaifinsu Amin Toddo ya bari a Kalmai, Billiri, Jihar Gombe a kwace su a hannun mahaifiyarsu (Kebba) ga magadan Amin Toddo, ma'ana ma su kara da wanda ake kara na hudu.
"Kotu mai alfarma ta hana wanda ake kara na 1, 2, da uku, ma'aikatansu ko abokansu daga shiga ko dasa bishiya a gonar da ke Ladongor, Kalmai Billiri Jihar Gombe."
Shi ma, lauyan wanda ake kara, Barista Ishaku David, ya shaidawa kotu cewa wanda ake kara na bukatar lokaci akan tuhumar da ake musu a kuma ba su lokaci don martani.
Kotun ta dage sauraren karar zuwa 27/04/2023.
Motar daukan yan firamari ya yi hadari a Legas
Ana Ramandan, Yan Addinin Gargajiya Sun Kai Hari Masallaci Sun Raunata Liman Da Wasu Mutane Da Dama A Osun
A wani rahoton, motar bas wacce ke jigilar yara yan makarantar firamari ta yi kundunbala bayan hadari a unguwar Surulere a Legas a ranar Alhamis.
Rahotanni sun nuna cewa dukkan yaran da ke motar da mai kula da su sun jikkata, shima direban ya yi rauni amma ya tsere.
Asali: Legit.ng