Yan Sanda Sun Cafke Wani Ɓarawo Da Aka Daɗe Ana Nema A Jihar Arewa, An Ƙwato Motocci Daga Hannunsa

Yan Sanda Sun Cafke Wani Ɓarawo Da Aka Daɗe Ana Nema A Jihar Arewa, An Ƙwato Motocci Daga Hannunsa

  • Dubun wani barawo ta cika bayan shiga hannun jami'an tsaro da su ka dade su na farutarsa
  • Jami'an yan sandan Jihar Nasarawa ne suka yi nasarar cafke barawon a babban birnin tarayya Abuja bayan sun bibiyi sahunsa
  • Hukumar yan sanda ta kama kayayyakin amfanin gida da yawa hannunsa, tare da mika shi kotu kafin a kammala bincike

Jihar Nasarawa - Rundunar yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wani mai laifi da ake zargi da sata a gidaje a karamar hukumar Karu da ke jihar, rahoton jaridar The Punch.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Lafia ranar Alhamis, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya ce wanda ake zargin ya dade a jerin wanda hukumar ke nema.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: An kafa tarihi, kasar Turai ta nada Firayinminista Musulmi a karon farko

Wanda ake zargi
Yan Sandan Nasarawa Sun Kama Barawo, Sun Kwato Motoci Biyu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

An bibiye shi tare da kama shi a babban birnin tarayya, Abuja, bayan namijin kokarin jami'an hukumar a cewar yan sanda, kamar yadda Tori.ng ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

''Ranar 27/03/2023 da misalin 12:30 na rama, an shigar da wani korafi a ofishin yan sanda na Karshi cewa, wasu da ba a san ko su waye ba, sun balle tare da sace kayan amfanin gida da su ka hadar da mota kirar Toyota matrix 2010 a wani gida da ke titin Modupe Olusola, Papaladna, da ke karamar hukumar Karshi.
''Bayan karbar korafin, an gudanar da kwakkwaran bincike akan lamarin. Kokarin yan sanda ya yi nasara a ranar 28/03/2023 lokacin da babban wanda ake zargi; Gabriel Okpe, 'namiji' mai shekaru 32 ya shiga hannu a Jikwoyi da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Yan Sandan Katsina Sunyi Musayar Wuta Da Yan Ta'adda, An Sheke Daya, An Kwato AK-47

''An kama wadannan kayan a wajensa a matsayin hujja: Toyata matrix mai lamba ABC 277 FV Abuja, Honda Accord mai lamba LC 699 EKY Lagos, talabijin filasma guda biyu, inji kirar Elpaq, fanka, karamar kwamfuta, microwave, tukunyar gas da abin turawa, waya ipad biyu, waya kirar Samsung, da sauran abubuwa.''

Nansel ya ce kwamishinan yan sanda, Maiyaki Baba, ya bada umarnin a tasa kayar wanda ake zargin zuwa kotu kafin su kammala bincike.

Jami'an Tsaro Sun Kama Yan Kungiyar Ta'addanci Da Ke Addabar Nasarawa Da FCT

A baya kun ji cewa cewa yan sandan FCT sun yi nasarar damke mambobin wata kungiya da ake zarginsu da adabar mutanen jihar Nasarawa da FCT, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164