"Yara Miliyan 17 Ke Fama Da Tamowa a Najeriya", Gwamnatin Tarayya
- Matsalar tamowa na ƙara ƙamari a ƙasar nan, gwamnatin tarayya ta bayyana adadin yaran da basu samun abinci mai gina jiki
- Wani sabon rahoto da ya fito ya bayyana cewa akwai aƙalla yara miliyan 17 dake fama da tamowa a ƙasar nan
- Wannan adadin na nufin Najeriya ce ta farko cikin ƙasashen Afrika dake fama da tamowa sannan ta biyu a duniya
Abuja- Gwamnatin tarayya da ƙungiyar abinci mai gina jiki ta duniya, Nutrition International (NI), sun bayyana cewa akwai aƙalla akwai yara miliyan 17 da basu samun abinci mai gina jiki a Najeriya.
Hakan ya sanya Najeriya ta zama ƙasa mafi yawan yara masu fama da tamowa a nahiyar Afrika, sannan ta biyu a duniya. Rahoton Leadership
An bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, wajen taro domin yin duba kan binciken da aka gudanar da ta hanyar amfani da Small Quantity Lipid-based Nutrient Supplements (SQLNS) da Multiple Micronutrient Powders (MNPs), a Abuja.
Da yake magana a wajen taron, darektan lafiya da abinci mai gina jiki na ministirin lafiya, Dr Binyerem Ukaire, yace rashin samun abinci mai gina jiki ya zama gagarumar matsala duk kuwa da kuɗin da ake narkawa akan hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ukaire ya bayyana cewa abubuwan da suke haifar da tamowa a Najeriya sun haɗa da rashin ciyar da jarirai da ƙananan yata abincin da ya dace, rashin samun abinci mai kyau mai ɗauke da sinadaran gina jiki, rashin samun wajen kula da lafiya, ruwa da tsafa, da kuma talauci.
"Gwamnatin tarayya tayi matuƙar ƙokari tare da haɗin guiwa da wasu ƙungiyoyi domin rage ƙarfin tamowa a ƙasar nan." Inji shi
A na shi ɓangaren, darektan Nutriton International (NI) na Najeriya, Dr Osita Okonkwo, yace tamowa ba matsala bace kawai wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, matsala ce wacce ke buƙatar a magance ta da gaggawa.
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Karin Albashin Ma'aikata
A wani labarin na daban kuma, gwamnatin tarayya ta amince s yiwa ma'aikata ƙarin albashin su.
Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, shine ya bayyana hakan, inda yace an kammala komai, abu ɗaya kawai ya rage yanzu.
Asali: Legit.ng