Yadda Iyayen Wani Yaro Da Ke Garanranba a Titi Suka Dawo Rayuwarsa Bayan Ya Samu Kyautar N2.5m

Yadda Iyayen Wani Yaro Da Ke Garanranba a Titi Suka Dawo Rayuwarsa Bayan Ya Samu Kyautar N2.5m

  • Wani matashi mai shekaru 12 da ke gararanba a titin Lagas tsawon shekaru biyar ya samu kyautar gida da kudi naira miliyan 2.5
  • Bayan labarin Saheed ya yadu yan kwanaki da suka gabata, mutane da dama sun nuna sha'awar son sauya labari da rayuwarsa
  • Yanzu ya bayyana cewa mutane da dama daga wurare daban-daban sun bayar da gudunmawa wanda shine aka tara miliyoyi kuma Saheed zai tafi UK karatu

Labarin wani matashin yaro da ke gararanba a titin Lagas tsawon shekaru biyar ya sauya cikin yan kwanaki kadan bayan labarinsa ya yadu a Instagram.

Yaron wanda ainahin sunansa Saheed ya samu kyautar kudi naira miliyan 2.5 kuma za a dauki nauyin karatunsa zuwa UK.

Saheed, iyayensa da wanda ya tallafa masa
Yadda Iyayen Wani Yaro Da Ke Garanranba a Titi Suka Dawo Rayuwarsa Bayan Ya Samu Kyautar N2.5m Hoto: @mufasatundednut
Asali: UGC

Iyayen yaron sun yi farin ciki da ganin cewa labarin ya shahara saboda sun yi nasarar ganin dan nasu kuma sun yi farin ciki da hawaye lokacin da suka samu labarin tagomashin alkhairin da dansu ya samu.

Kara karanta wannan

Wata Uwa Ta Koka Bayan Karamin Danta Ya Zubar Da Madarar N16k a Kasa, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

A wani bidiyo da ya yadu, an gano uwar yaron tana kuka tare da godiya ga masu amfani da soshiyal midiya wadanda suka sa wallafar yadu da kuma hada masu kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun cika da farin ciki cewa anyi amfani da kafar intanet ta hanya mai kyau wajen inganta rayuwar yaron.

Bidiyon na dauke da take kamar haka:

"Wadannan sune iyayen Saheed, ya kasance yana zaune da mahaifiyarsa kafin mahaifiyar ta gaza rike shi saboda abubuwa sun yi wahala don haka ta mayar da shi ga mahaifinsa kuma a cikin haka ne aka zarge shi da sace naira 200 kuma yana tsoron cewa za a yi masa duka don haka ya gudu daga Ilorin zuwa Ibadan sannan ya tafi Lagas cikin yan watanni kadan Godiya ga Allah cikin yara 15 da na gani a titi na zabe shi kuma ina godiya ga Allah da kuma wadanda suka taimaka da daukar nauyin Saheed saboda an ba hsi naira miliyan 2.5 za mu samawa mahaifiyarsa wajen zama, shagon da zai kawo mata kudaden shiga sannan za a dauki nauyin karatun Saheed zai tafi UK nan da yan watanni."

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Samu Cikin Fari Tana Da Shekaru 54, Allah Ya Azurta Ta Da Yan Uku a Bidiyo

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@swagtohbad ya yi martani:

"Ma shaa Allah! Hakan ya yi kyau. Saheed zai ma rigani shiga UK. Wallahi ina wasa da rayuwana."

@samvail_ ya ce:

"Kalli yadda gayen yake magana cike da nauyin zuciya. Wannan gayen dan kwarai ne. Allah ya yi wa duk wadanda suka ba da gudunmawa albarka."

@chrismelbourne ta rubuta:

"Wanda zai taimakeka ba zai wahalar da kai ba."

Ma'aurata sun gano su yan uwa ne bayan shekaru 17

A wani labari na daban, ma'aurata sun bankado ashe akwai alaka ta jini a tsakaninsu bayan sun shafe shekaru 17 da aure. Sai dai sun ki karbar shawarar mutane na cewa su rabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng