“Ba Za Mu Rabu Ba”: Ma’aurata Sun Ki Karbar Shawara Bayan Sun Gano Suna Da Alaka Ta Jini

“Ba Za Mu Rabu Ba”: Ma’aurata Sun Ki Karbar Shawara Bayan Sun Gano Suna Da Alaka Ta Jini

  • Wasu ma'aurata da suka shafe tsawon shekaru 17 da aure sun gano suna da alaka bayan matar ta yi gwaji kuma mutane sun basu shawarar rabuwa
  • A rahoton, matashiyar ta bayyana cewa suna da yara uku tare kuma basu taba sanin su yan uwa bane sai bayan shekaru 17 da aure
  • Wannan abu da suka gano ya sa sun yi fice bayan matar ta sanar da labarin a TikTok amma kuma ya ja masu suka

Wani miji da mata da suka shafe tsawon shekaru 17 suna rayuwa tare sun gano cewa suna da alaka ta jini.

Dailymail ya rahoto cewa ma'auratan sun yi soyayya na watanni hudu kacal kafin suka shiga daga ciki.

Mata da miji masu dangantaka
“Ba Za Mu Rabu Ba”: Ma’aurata Sun Ki Karbar Shawara Bayan Sun Gano Suna Da Alaka Ta Jini Hoto: TikTok/Dailymail
Asali: UGC

Celina Quinones, matar, ta yi gwajin kwayoyin halitta wato DNA kuma ta haka ne ta gano gaskiya game da tarihin ahlinsu.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Mata Mai Mazaje 2 Ta Magantu Kan Yadda Ta Hadu Da Mijinta Na Biyu

Kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yara uku kenan a cikin haka ne na gano cewa muna da alaka. Na yi gwajin kwayoyin halittana wato DNA ina ganin a 2016 kuma kwarai da gaske akwai ban mamaki saboda na ce 'masoyi' muna da alaka shin ya kamata mu kasance tare? Wannan abun mamaki ne. Ba zan sauya shi saboda duniya ba...danuwamiji da mata har abada! Akwai dalilin da yasa ma'aurata ke kama da juna. Ina nan ina wayar da kai."

Jama'a sun soke su

An rahoto cewa Celina da mijinta sun sha caccaka sosai daga mutane bayan sun sanar da duniya cewa suna da alaka ta jini amma ba za su rabu ba.

Mutane da dama sun ba su shawarar cewa ya kamata su raba auren amma sun bayyana cewa sun rigada sun yanke shawara.

Celina ta dage cewa auren zai ci gaba saboda sun zuba jari sosai a ciki na tsawon shekaru 17.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

Ta ce:

"Sai na rabu da shi saboda bamu sani ba. Kawai sai na fadawa yaranmu cewa iyayensu basa tare kuma saboda ra'ayin wasu mutane. A'a nagode za mu kasance yan uwa masu tsayawa tare, ma'aurata kuma masoya har abada. Yanzu ku je ku tsoma bakinsu a wasu abubuwan."

Uba ya shayar da dansa ta hanyar yi masa wayo

A wani labarin, wani uba ya kirkiro dabarar shayar da dansa bayan matarsa kuma mahaifiyar yaron ta fita.

Mutumin dai ya nemo hoton fuskar matar tasa sannan ya daura a nashi tare da manna fidan madaran yaron a kirjinsa ka ce nono yake shayar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng