MURIC: Kungiyar Musulmi Ta Ce Jami'an Tsaro Su Ja Kunnen Datti Kan Cewa Kada A Rantsar Da Tinubu
- Kungiyar MURIC, mai rajin kare hakkin musulmi a Najeriya ta yi kira ga hukumomin tsaro su ja kunnen Datti Baba-Ahmed kan cewa kada Alkalin Alkalai na kasa, CJN, ya rantsar da Bola Ahmed Tinubu
- Baba-Ahmed, yayin jawabi kan batun rashin samun kuri'u kashi 25 a Abuja da Tinubu dan takarar APC bai yi ba, ya yi kira ga CJN kada ya rantsar da Tinubu don hakan ya saba kundin tsarin mulki
- Farfesa Akintola, shugaban kungiyar MURIC ya ce kalaman na Baba-Ahmed karan tsaye ne ga doka kuma tamkar kira na ga sojoji su yi juyin mulki don haka ya bukaci hukumomin tsaro su gargadi Datti
Kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta ce ya kamata a ja kunnen dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed kan cewa babu zababben shugaban kasa.
Yanzu-Yanzu: DSS Ta 'Gano' Manyan Yan Siyasa Da Ke Shirin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Gabanin Mika Wa Tinubu Mulki
Farfesa Ishaq Akintola, babban direktan MURIC, ya ce akwai 'ganganci' cikin kalaman na Baba-Ahmed, The Cable ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Baba Ahmed ya bukaci Olukayode Ariwoola, babban alkalin alkalan Najeriya, kada ya rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu, yana mai cewa hakan saba kundin tsarin mulkin kasa ne.
Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tsokaci kan gaza samun kuri'u kashi 25 na birnin tarayya Abuja a zaben shugaban kasa na watan Fabrairu.
Fasarar sashin doka da ya yi magana kan hakan na cikin abubuwan da za a tafka muhawara a kansa a kotun zabe.
Kalaman Datti tamkar kira ne ga sojoji su yi juyin mulki - Farfesa Akintola
Akintola ya ce kalaman Baba-Ahmed kan batun daidai ya ke da cewa a yi juyin mulkin soja.
Ya yi kira ga shugabannin addini da wadanda abin ya shafa su 'ja kunnensa' kan furta maganganu da ka iya 'tada zaune tsaye.'
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce:
"Hakan na nufin tada kayan baya da neman juyin mulkin soja. Babu wanda ya yi imani da dimokradiyya da zai furta hakan. Idan jami'an tsaro ba su gargade shi da irinsa ba, ba su cika aikinsu.
"Wannan mika mulkin na da muhimmanci. Kada a yi sakaci da kowa.
"Halastaciyyar hanyar canja gwamnati shine ta hanyar zabe da aka yi. Duk wata hanya daban bata halasta ba kuma saba doka ne."
MURIC ta yi kira ga Datti 'ya bi tsarin doka' ta kuma yi gargadi game da yin zanga-zanga kan batun da ake shari'arsa a kotu.'
Asali: Legit.ng