"Biyayya Na Ke Wa Mijina", Matar Da Aka Kama Da Ƙanwarta Da Ganyen Wiwi a Jihar Katsina
- Hukumar yaki da miyagun kwayoyi, NDLEA, a Katsina ta kama wasu mata biyu (yaya da kanwa) kan mallakar miyagun kwayoyi
- Rabi Musa, daya daga cikin matar da aka kama ta ce mijinta ne ya kawo kwayoyin ita kuma ta karba saboda ta yi masa biyayya
- Mohammed Bashir, kwamandan hukumar NDLEA na Katsina ya shawarci iyaye su rika bukatar gwajin kwaya daga samarin da za su auri yayansu
Jihar Katsina - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta yi holen yaya da kanwa da mijin daya cikinsu kan mallakar kiligram 6 na ganyen wiwi, rahoton The Punch.
Kwamandan hukumar yaki da kwayoyin a jihar Katsina, Mohammed Bashir, ya fada wa manema labarai cewa wata, Rabi Musa, yar shekara 45, an kama ta da kilogram uku na ganyen wiwi din.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce Rabi na taya mijinta, wanda yanzu ana nemansa, wurin sayar da haramtaciyar kwayar tare da yar uwarta, Zainab Musa da mijinta.
Ya ce an kama Zainab da mijinta kuma saboda samunsa da wani kilogram uku na haramtaciyar kwayar.
Bashir ya ce kama Rabi ya yi sanadin kama sauran biyun da ake zargi kuma ya bada tabbacin za a kamo mijinta da ya tsere.
Ya ce an fara bincike da nufin gurfanar da mutanen ukun da aka kama.
Yawaitar mutuwar aure a Katsina na da alaka da ta'amulli da kwayoyi - Bashir
Hakazalika, ya alakanta yawaitar mutuwar aure a jihar Katsina da ta'amulli da miyagun kwayoyi ya yi kira ga iyaye su rika umurtar yin gwajin kwayoyi kan wadanda yayansu za su aura.
Ya kuma ce iyayen su rika bukatar satifiket din gwajin kwayoyi daga mazan da yayansu mata za su aura a maimakon biye wa kudi.
Biyayya na ke yi wa miji na - Rabi
A yayin da ta ke amsa tambayoyi, Rabi, yar shekara 45 ta amsa aikata laifin amma ta ce biyayya kawai ta ke wa mai gidanta.
Ta roki a yi mata afuwa kuma ta shawarci iyaye su rika bincike kan mazajen da suka zo neman auren yayansu mata.
An kama mai sarautar gargajiya da tubabben dan ta'adda kan safarar miyagun kwayoyi
Hukuma mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta kama wani tubabben dan ta'adda, Alayi Madu, da wani mai sarautar gargajiya, Baale Akinola Adebayo kan zarginsu da safarar miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng