Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rijiyar Hakar Man Fetur a Jihar Nasarawa

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rijiyar Hakar Man Fetur a Jihar Nasarawa

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar rijiyar haƙar man fetur a Arewacin Najeriya
  • Shugaba Buhari yace rijiyar ba ƙaramin cigaba za ta samar ba ga ƙoƙarin ƙasar nan na samun isashshen makamashi
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa kakar al'ummar dake kusa da wajen ta yanke saƙa domin za su amfana sosai

Abuja- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da rijiyar haƙo man fetur ta Ebenyi-A, wacce take a ƙaramar hukumar Obi, a jihar Nasarawa.

Bikin ya kasance shine karon farko da aka fara ayyukan haƙar mai a kwamin kogin Benue na tsakiya. Rahoton The Cable

Rijiyar mai
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rijiyar Hakar Man Fetur a Jihar Nasarawa Hoto: The Cable
Asali: UGC

Da yake magana a wajen taron ranar Talata, shugaba Buhari yace taron wani gagarumin cigaba ne a haƙar man fetur da iskar gas da Najeriya ke yi.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Kungiyar Kwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba CBN Wani Sabon Wa'adi

"Wannan ya zo daidai da gano albarkatun mai a yankin Kolmani na kwamin kogin Benue na sama. Ina farin cikin sanar da ku cewa ana cigaba da ayyuka a Kolmani domin samar da man fetur wanda zai shiga kasuwa." Inji shi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari yace fafutukar haƙo man fetur ɗin da ake yi zai samar da cigaba ga al'umma da kuma ƙara ƙarfin makamashin da ƙasar nan take da shi.

Ya ƙara da cewa al'ummar dake yankin za su amfana daga kuɗin shigar da za a riƙa samu daga haƙar man, wanda hakan zai kawo cigaba sosai a yankin. Rahoton Vanguard.

Da yake magana a wajen taron, shugaban kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC), Mele Kyari, ya bayyana cewa a shekarar 2010 aka fara neman man fetur a kwamin kogin Benue.

“Yau mun fara rijiyar farko a kwamin kogin Benue na tsakiya, a yayin da kuma muke cigaba da bin umurnin shugaban ƙasa na nemo man fetur a yankunan da ba teku ba." Inji shi

Kara karanta wannan

"Gwamnati a Ƙarƙashin Jagorancin Tinubu Zata Kasance Mai Tasiri ga Rayuwar Ƴan Najeriya" – Buhari

Kyari yace tagomashin da za a samu daga binciko ma'adan zai taimakawa burin da ƙasar ke da shi na ƙara yawan makamashin ta ganga biliyan 37 da ke ajiye zuwa ganga biliyan 50 nan gaba.

Ya ƙara da cewa zai ƙara yawan man fetur ɗin da ake samarwa zuwa ganga miliyan uku a rana.

Kungiyar Kwadago Ta Janye Yajin Aiki, Ta Ba CBN Wani Sabon Wa'adi

A wani labarin na daban kuma, ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aikin da ta ƙudiri aniyar yi a faɗin ƙasar nan kan ƙarancin kuɗi.

Ƙungiyar tace ba gabaɗaya ta haƙura ba inda ta ba CBN wani sabon wa'adi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng