Mutum 24 Sun Mutu Yayin Da Wata Babban Mota Da Ta Tashi Daga Zaria Zuwa Legas Ta Yi Haɗari
- Wani mummunan hadarin mota ya yi sanadin salwantar rayukan mutane 24 a Jihar Niger
- Hadarin da ya auku da daren Litinin da ya rutsa da wata babbar motar daukar kaya dauke da fasinja daga Zaria zuwa Lagos dauke da mutane 87
- Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta tabbatar da faruwar lamarin tare da shaida cewa an kwashe wanda su ka jikkata zuwa asibiti yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin adana gawa na Kutigi
Jihar Niger - Wani hadarin mota ya yi sanadin salwantar rayuka 24 da daren Litinin 27 ga watan Maris a karamar hukumar Lavun da ke Jihar Niger, rahoton The Punch.
Babban motar da ke dauke da fasinjojin tana kan hanyarta na zuwa Legas ne daga Zaria kuma akwai mutane 87 a cikinta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Babban kwamandan shiyya na Jihar Niger a Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa, FRSC, Kumar Tsukwan, shi ne ya bayyana haka a rahoton masaniyar farko na hadari ya kuma bawa wakilin majiyarmu, hadarin ya faru a kauyen Etsu Woro.
''Fasinja 24 da ke tahowa daga Zaria zuwa Lagos sun mutu a hadarin da ya hada da babbar mota dauke da fasinja 87 a kauyen Etsu Woro da ke karamar hukumar Lavun a Jihar Niger," in ji shi.
Adadin mutanen da ke cikin motar
Tsukwan ya ce akwai maza 17, mata hudu da kananan yara 4 sun mutu a babbar motar Lone Sino a hadarin tare da karin 45 da su ka ji rauni daban-daban aka garzaya da su asibiti don karbar magani.
Ya kara da cewa an kai gawarwakin zuwa dakin ajiye gawa.
Ya ce:
''An kwashe wanda abin ya shafa daga wajen da hadarin ya faru zuwa babban asibitin Kutigi don karbar magani yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin adana gawa na Kutigi.''
Hatsarin mota ya yi sanadin rasa rayyuka biyu a jihar Jigawa
A wani rahoton mai kama da wannan kun ji cewa wasu mutane biyu sun rasu a wani hadarin mota da ya afkuw a hanyar Jahun zuwa Kiyawa a Jihar Jigawa.
Adamu Shehu, mai magana da yawun hukumar tsaro ta NSCDC na jihar Jigawa ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng