An Maka Wani Mutum da Ya Haifi ’Ya’ya Sama da 500 Ta Hanyar Ba da Gudunmawar Maniyyinsa a Kotu

An Maka Wani Mutum da Ya Haifi ’Ya’ya Sama da 500 Ta Hanyar Ba da Gudunmawar Maniyyinsa a Kotu

  • Wani labari mai daukar hankali ya karade kafafen yada labarai na mutumin da ke ba da gudunmawar maniyyi
  • Mr. Meijer zai fuskanci tuhumar kotu kan zargin wuce gona da iri wajen ba da gudunmawar maniyyinsa
  • A karar da aka shigar, an bayyana abubuwan da ake so kotun ta tursasa shi ya yi don kaucewa matsaloli

Kasar Jamus - An maka mutumin da ya yi sanadiyyar zuwan yara sama da 550 duniya a kotu bisa tsoron abin da ka iya biyo baya na auratayya tsakanin yaran, Telegraph ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, Jonathan Jacob Meijer, wanda ke ba da maniyyinsa ga wadanda ba sa haihuwa a matsayin gudunmawa zai iya fuskantar fushin kotu.

Mutumin mai shekaru 41 na fuskantar tuhuma ne da wata gidauniyar kasar Netherlands mai suna Donorkind Foundation, inda ta nemi a hana shi ci gaba da ba da maniyyinsa ga jama’a.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu 'yan kutse sun shiga jihar Arewa, sun hallaka masunta 4 da magidanci

An kai mutumin da aka haifi yara 550 ta sanadiyyarsa
Mr. Meijer kenan, mai ba da gudunmawar maniyyi | Hoto: barristerng.com
Asali: UGC

Hakazalika, gidauniyar ta zarge shi da shirga karya bisa bayyana adadin yaran da ya yi sanadiyyarsu zuwa duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka maka Mr. Meijer a kotu

Wata mata ‘yar asalin kasar Jamus ce ta shigar da karar, wacce aka ce ita ma ya ba ta gudunmawar maniyyin a 2018.

A ka’ida, mai ba da gudunmawar maniyyi zai bayar ne sau 25, ko kuma ya ba mata 12 don rage yaduwar auratayya tsakanin ahali daya da kuma matsalolin kwakwalwa ga ‘ya’yan da aka haifa, inji wani asibitin Jamus.

A cewar matar da ta shigar da karar:

“Idan da na san ya yi sanadiyyar zuwa yara sama da 100 duniya da ba zan zabe shi ba. Idan na tuna illar da hakan ke tattare dashi ga dana ba sai na ci ciwo a ciki na.”

Abin da ake so kotu ta yi masa

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Gidauniyar Donorkind Foundation tana neman kotu ta hana Mr Meijer ci gaba da ba da gudunmawa ga jama’a, sannan a binciko asibitin da yake kai gudunmawar, rahoton jaridar Express.

Hakazalika, gidauniyar na neman a lalata dukkan maniyyin da Mr. Meijer ke dashi a ajiye a matsayin na gudunmawa, sai dai ga matan da a baya ya taba ba gudunmawar.

A halin da ake ciki, Mr Meijer na jerin mutanen da ke cikin bakin jadawalin masu ba da gudunmawar maniyyi ba bisa ka’ida ba a Jamus da ma sauran kasashen waje irinsu Denmark da Ukraine.

Hakazalika, gidauniyar ta bayyana cewa, mutumin yana ci gaba da bayyana halinsa na ba da gudunmawa a kafafen sada zumunta.

Wani rahoto ya ce, bincike ya ce direbobi masu tafiyar dogon zango ka iya fuskantar karancin maniyyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.