Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ce Za a Kammala Sauran Zabukan Najeriya da Suka Rage a Ranar 15 Ga Afrilu
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar karasa zabukan da aka yi ba a kammala ba a Najeriya
- A ranar 15 ga watan Afrilu ne za a karasa zabukan, kamar yadda INEC ta bayyana a yau Litinin 27 ga watan Maris
- An samo tsaiko a wasu bangarori daban-daban an Najeriya, an soke sakamako, an kuam dage sanar da sakamakon zabe
FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanya ranar da za ta kammala zabukan da suka rage ba a yi su ba a Najeriya na bana.
Hukumar ta ce, za a kammala sauran zabukan gwamna, na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi ne a ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa.
Idan baku manta ba, an samu tsaiko a Najeriya, har ta kai aka dage zabe ko soke shi a wasu yankuna daban-daban na kasar nan.
A wasu yankuna da jihohin a Najeriya, an samu tsaikon da ya kai ga zubar da jini, misali kamar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da INEC ke cewa game da sake zabe a wasu yankuna
A sanarwar da INEC ta fitar a ranar Litinin 27 ga watan Maris, ta ce:
“A taron da ta gudanar a yau, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkan zabukan gwamnoni, na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi da ba a yi ba a a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023.”
Ya zuwa yanzu, hukumar bata bayyana sanarwar inda za a yi zaben ba a hukumance, amma ta ce za ta ba da bayani nan ba da jimawa ba.
INEC ta ayyana sakamakon zaben Adamawa ‘Inconclusive’
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
A wani labarin, kuma zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa, bata amince da sakamakon zaben jihar Adamawa da aka gabatar mata ba a makon da ya gabata.
Wannan ya faru ne sakamakon tsaiko da jinkirin da aka samu wajen tattara sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da muke ciki.
Hukumar ta bayyana cewa, za a sake yin zaben a wasu yankunan jihar, inda ta bayyana cewa za ta sanar da lolacin bayan duba cikin tsanaki.
Asali: Legit.ng