Rikici Ya Barke a Tsakanin 'Yan Ta'addan ISWAP, Babban Kwamandan Ya Sheke Mataimakin Sa
- Kwamandan ƙungiyar ƴan ta'addan Islamic State For West Africa (ISWAP), Abu Muhammed ya halaka mataimakin sa
- Kwamandan ya zargi mataimakin sa wajen nuna sakaci wanda ya sanya sojoji suka halaka mayaƙan sa da dama
- Abu Muhammed ya kuma sha alwashin ɗaukar fansar wannan kisan kiyashin da sojoji suka yiwa mayaƙan sa
Jihar Borno- Kwamandan ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP, Abu Muhammed, ya halaka mataimakin sa, Abu Darda, a dalilin barin da yayi sojoji suka farmaki sansanin su a ƙauyukan Mukdolo da Bone.
Farmakin na sojojin dai ya sanya an halaka mayaƙan ƙungiyar 41 ciki har da Abu-Zahra Munzir.
Zagazola Makama wani masani kan lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, ya samo cewa fusataccen kwamandan ya sheƙe Abu Darda ne a gaban sauran mayaƙan a ƙauyen Kajeri Dogumba cikin ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Majiyoyin sirri sun gayawa Zagazola Makama cewa Abu Muhammed ya zargi Abu Darda da jagorantar harin da ba ayi nasara ba a ranar 19 ga watan Maris a Mafa wanda yayi sanadiyyar halaka ƴan ta'addan da dama da kuma ƙwace motocin su guda biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kwamandan yace motoci uku kawai gare su amma gazawar Abu Darda ta sanya sojojin suka kwace su, inda yayi nuni da cewa ya kasa lura lokacin da sojoji suka biyo sawun sa suka farmake su suna barci a sansanin.
Kwamandan ya bayyana cewa yaji zafi ne sosai saboda sojojin sun halaka mayaƙan sa da dama, sun ƙona kayan abincinsu da kuma wasu sabbin kayan ɗaki na shirin auren sa da ya siyo.
Kwamandan wanda yanzu haka yake tattaro kan mayaƙan sa a Kajeri Dogumba, Bula Yagana Aliye a ƙaramar hukumar Mafa, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mayaƙan sa.
Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara
Dakarun sojojin Najeriya a Operation Hadin Kai, sun dira a maɓoyar ƴan ta'adda ISWAP a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno, inda suka halaka ƴan ta'adda 41 ciki har da wani kwamanda Abu Zahra.
Yan Sanda Sun Kama Mutane 79 da Suka Ta Da Yamutsi a Zaben Gwamnan Sakkwato
A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun yi ram da mutane da dama masu tayar da.zaune tsaye a lokacin zaɓen gwamnan jihar Sokoto.
Ƴan sanda sun same su da aikata laifuka daban-daban da suka saɓawa doka a lokacin zaɓen.
Asali: Legit.ng