Akwai Yiwuwar CBN Ya Kakaba Amfani da Manhajar eNaira Saboda Karancin Kudi a Najeriya
- Har yanzu ana ci gaba da fama da karancin yawon sabbin Naira a Najeriya, yayin da CBN ya saki tsoffin kudaden kasar
- Rahoto ya ce, CBN ya fara kokarin tabbatar da ana amfani da manhajar eNaira, inda ya fara horar da masu sana’ar POS kan amfani da ita
- An kuma gano cewa, wasu manyan ma’aikatan banki sun ce, kusan wata guda kenan rabonsu da ganin sabbin kudade daga CBN
A kwanan nan, ‘yan Najeriya sun shaida yadda karancin yaduwar sabbin Naira yake, inda ‘yan kasar ke ci gaba da fama da kashe tsoffin kudaden da kotun koli yace a ci gaba da amfani dasu.
Wannan ya faru ne a daidai lokacin da babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna su fara aiki a ranakun Asabar da Lahadi.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, CBN ya tsaya da rarraba sabbin takardun Naira ga bankunan kasuwanci a kasar, hakan ya jawo karancinsu a ko’ina.
An ga bankuna da yawa a kasar na makare injunan ATM dinsu da tsoffin takardun Naira domin biyan bukatun kwastomominsu a kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Babu sabbin Naira a kasa
Wasu bankunan kuma, sun ce basu sake jin duriyar sabbin takardun Naira ba daga CBN tun watan jiya, duba da karuwar yaduwar tsoffin kudaden.
An ruwaito yadda wasu majiyoyi ke cewa, akwai yiwuwar CBN ya kakaba amfani da manhajar eNaira a matsayin dole yayin da bankin ya fara yiwa masu POS horon amfani da ita.
A cewar majiyar, ya zuwa yanzu dai ba a fara horar da ma’aikatan banki game da sarkakiya da saukin amfani da manhajar ba.
Anfami da eNaira ya ninku sau ribi 12
Jaridar Bloomberg ta ruwaito cewa, adadin masu amfani da manhajar eNaira ya karu sau ninki 12 zuwa miliyan 13 tun watan Oktoban 2022, inda darajar hada-hadarsa ya kai 63% zuwa N22bn a 2023.
Mukaddashin daraktan sashen yada labarai na CBN, Isa Abdulmumin ya ce, bankuna na samun wani adadi ne kadai na tsabar kudi don rabawa kwastomominsu.
Abdulmumin ya ce, CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci da su makara na’urorinsu an ATM da kudi, kana su fito aiki a ranar karshen mako.
Kakakin na CBN ya kara da cewa, gwamnan bankin, Godwin Emefiele zai jagoranci tawagar tabbatar da ana bin umarninsa a fadin kasar.
A makin jiya, an kama masu sana'ar POS da ke saye da siyar da takardun Naira ba bisa ka'ida ba kan farashi mai tsada.
Asali: Legit.ng