Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Oladipo Diya, Ya Mutu

Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Oladipo Diya, Ya Mutu

  • Tsohon gwamnan jihar Ogun a mulkin soja kuma tsohon mataimakin Abacha, Janar Oladipo Diya mai ritaya, ya rasu
  • A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Barista Oyesinmilola Diya, marigayin ya cika ne yau Lahadi 26 ga watan Maris
  • A shekarar 1997 aka yanke masa hukuncin kisa bisa zargin cin amanar kasa amma ya kubuta bayan mutuwar Abacha

Tsohon Janar a rundunar sojin Najeriya, Janar Oladipo Diya mai ritaya, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 78 a duniya.

The Cable ta rahoto cewa hakan na kunshe a wata sanarwa da iyalansa suka fitar mai ɗauke da sa hannun Oyesinmilola Diya, a madadin sauran iyalan baki ɗaya.

Oladipo Diya.
Marigayi Janar Oladipo Diya mai ritaya Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Marigayi Diya, ya yi aiki a matsayin shugaban rundunar sojin Najeriya baki ɗaya a zamanin mulkin Soji na tsohon shugaba ƙasa, Sani Abacha, daga 1994 zuwa 1997.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Tarihi ya nuna cewa an kama Diya kuma aka yanke masa hukuncin kisa bisa zargin cin amanar ƙasa a shekarar 1997, amma ya kubuta bayan mutuwar Abacha a 1998.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwan da Barista Oyesinmilola Diya, ya fitar ta ce tsohon shugaban dakarun tsaron ya cika ne da sanyin safiyar ranar Lahadi 26 ga watan Maris, 2023.

Shi ne mutum na biyu mai karfin faɗa a ji a zaman mulkin Abacha wanda a yanzu zamu iya kiransa mataimakin shugaban ƙasa. Sanarwan ta ce:

"A madadin iyalan gidan Diya na nan gida Najeriya da waje, muna sanar da mutuwar masoyin mijinmu, mahaifinmu, kakanmu, ɗan uwa, Janar Donaldson Oladipo Oyeyinka Diya (mai ritaya) GCON, LLB, BL, PSC, FSS, mni."
Mahaifin mu ya riga mu gidan gaskiya da safiyar Lahadin nan 26 ga watan Maris, 2023. Dan Allah ku taimaka mana da addu'a yayin da muke cikin yanayin baƙin ciki da jimamin wannan rashi."

Kara karanta wannan

25 Sun Mutu, 10 Sunji Munanan Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Bauchi

"Zamu sake fitar da sanarwa kan rasuwar idan bukatar hakan na ta so nan gaba kuma a lokacin da ya dace."

Mamacin ya kasance tsohon gwamnan jihar Ogun na mulkin soji daga watan Janairu, 1984 zuwa watan Agusta 1985, kamar yadda daily Trust ta rahoto.

An Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamnan Imo Na Jam'iyyar LP

A wani labarin kuma Ɗan takarar gwamnan jihar Imo a inuwar Labour Party ya rasu jim kaɗan bayan dawowa daga taro a Abuja

Wani aboki na kusa ya ce ɗan siyasan wanda ya rika ya sayi Fam ɗin fafatawa a zaben fidda gwani ya mutu da yammacin ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262