Yanzu-Yanzu: CBN Ya Umurci Bankuna Da Su Fito Aiki a Ranakun Karshen Mako

Yanzu-Yanzu: CBN Ya Umurci Bankuna Da Su Fito Aiki a Ranakun Karshen Mako

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankuna da su buɗe rassan su a ranakun ƙarshen mako
  • Babban bankin ya kuma rabawa bankunan isassun takardun kuɗi waɗanda za su rabawa kwastomomin su
  • Bankin ya bayar da tabbacin cewa matsalar ƙarancin kuɗi na daf da zuwa ƙarshe domin ya antayo isassun kuɗi ga bankuna

Abuja- Babban bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da fito da takardun kuɗi daga ma'ajiyar sa domin rabawa ga bankuna a faɗin ƙasar nan a shirin da yake yi na ganin an samu wadatuwar takardun kuɗin a faɗin ƙasar nan.

Babban bankin CBN ya kuma umurci dukkanin bankunan kasuwanci da su fito su yi aiki a ranakun ƙarshe sati wato Asabar da Lahadi. Rahoton Leadership

Emefiele
Yanzu-Yanzu: CBN Ya Umurci Bankuna Da Su Fito Aiki a Ranakun Karshen Mako Hoto: The Guardian
Asali: Getty Images

Darektan rikon ƙwarya na fannin watsa labarai na CBN, Dr. Isa AbdulMumin, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ashsha: Jami'an EFCC Sun Yi Ram Da Malamin Addini Mai Yahoo-Yahoo a Arewacin Najeriya

Dr AbdulMumin ya bayyana cewa an ba bankuna takardun kuɗi masu yawa domin cigaba da rabawa kwastomomin su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sa, babban bankin na CBN ya kuma umurci bankuna da su sanya kuɗi a injinan ATM ɗin su, sannan kuma su yi aiki a ranakun ƙarshen sati.

“Rassan bankunan kasuwanci za su buɗe a ranakun Asabar da Lahadi domin biyan buƙatun kwastomomi na samun cash." Inji shi

Ya kuma ƙara da cewa, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da kan shi zai jagoranci tawaga wacce zata duba taga ko bankuna na bin wannan umurnin a yankuna daban-daban na ƙasar nan.

A dalilin hakan, sai ya roƙi ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan wanda suka yi domin wannan raɗaɗin da ake ciki ya kusa zuwa ƙarshe a dalilin antayo kuɗin da bankin yayi yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ekweremadu Bisa Zargin Safarar Sassan Jiki

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ma'aikacin banki a birnin Katsina, wanda ya tabbatar da cewa umurnin babban bankin Najeriyan ya iso gare su, kuma za su fito aiki a ranakun Asabar da Lahadi.

Ma'aikacin bankin ya kuma bayar da tabbacin cewa bankin na su ya samu isassun kuɗaɗe daga CBN waɗanda zai rabawa kwastomomin sa, inda yace tun a yau Juma'a ma bankin su ya fara ba mutane kudaɗe.

Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen da bankin na su ya samu daga hannun CBN tsaffin kuɗaɗe ne.g

Babban Bankin Najeriya (CBN) Zai Sako Tsofaffin Takardun Kudi

A wani labarin na daban kuma, babban bankin Najeriya (CBN) zai sako tsaffin kuɗin dake ajiye a hannun sa.

Babban bankin yace zai yi hakan ne domin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suke ckki saboda ƙarancin kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng