Yan Daba Sun Tare Zababben Dan Majalisa A Arewa, Sun Cinnawa Motarsa Wuta
- Wasu miyagu da ba a san ko su wanene ba sun kai wa zababben dan majalisa na Gbemacha a Benue, Aondona Dajoh hari
- Wani na kusa da Dajoh, wanda ya magantu kan lamarin ya bada bayani kan yadda maharan suka rika bin zababben dan majalisar a mota har ta kai ga ya tsere ya bar musu motar
- Bayan maharan sun gano cewa Dajoh ya fice daga motarsa a wani wuri ya tsere, sun cinna wa motar wuta sannan suka tafi
Jihar Benue - Yan daba sun kai wa Aondona Dajoh, zababben dan majalisa mai wakiltar Gbemacha, wanda aka fi sani da Gboko West a majalisar jihar Benue karkashin jam'iyyar APC.
Dajoh, wanda maharan suka suka cinna wa motarsa wuta a daren ranar Alhamis misalin karfe 10 na dare, amma, ya tsere da lafiyarsa, rahoton Leadership.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kakakin yan sandan jihar Benue, Catherine Anene, da aka tuntube ta a jihar tarho ta tabbatar da harin da aka kai wa zababben dan majalisa.
Kakakin yan sandan ta ce:
"Duk da ya tsira daga harin, an kona motarsa kurmus."
Leadership ta rahoto cewa daya daga cikin makusantan Dajoh, wanda baya son a ambaci sunansa a jarida, ya ce zababben dan majalisar ya zauna tare da wani abokinsa a ranar Alhamis bayan taro da dattawan Gbemacha a gidansa, sunan suka rabu kowa ya kama gabansa yayin da shi Dajoh ya kama hanyar zuwa Adekaa, wani gari a Gboko.
Ya ce:
"A hanyarsa na dawowa daga Adekaa, misalin karfe 10 na dare ya lura wani mota na binsa a baya, bai gamsu ba, hakan yasa ya kara gudun motarsa don kada su tare shi.
"Nan take da suka ga ya kara gudu, motar da ke bayansa sun fara haska masa fitila kuma ya kara gudu ya tafi wani wuri da ya ga mutane da yawa kusa da Asibitin Gyado ya ajiye motarsa ya tsallake katanga ya tsere.
"Da motar ta iso inda ya yi fakin din motarsa, sun sako da sauri suka tare motarsa da suka gano babu kowa a ciki sai suka cinna wa mota wuta."
Mota dauke da yara yan firmari ya yi hadari a Legas
A wani rahoto, wani mota dauke da yan firmari a Legas ya yi hadari a unguwar Surulere a Legas.
Rahoto sun ce yaran da ke motar da mai kula da su sunyi rauni, shima direban ya yi rauni amma ya tsere.
Asali: Legit.ng