Wike Ya Ba Wa AIT/Ray Power Awa 48 Su Fice Daga Ribas, Ya Bada Dalili

Wike Ya Ba Wa AIT/Ray Power Awa 48 Su Fice Daga Ribas, Ya Bada Dalili

  • Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya fada wa Daar Communication, mamallakin AIT/Ray Power, su bar ofisoshinsu cikin awa 48
  • A cikin wata sakon gargadin kora daga gida da sakataren ma'aikatar ayyuka na jihar ya saka wa hannu, Ebere Dennis Emenike, ya ce za a rushe ginin cikin kwana 2
  • A cewar sanarwar ta gargadi, za a rushe ginin da kafar watsa labaran ta ke a unguwar Ozuoba a Fatakwal, babban birnin jihar

Fatakwal, Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bukaci Daar Communication, mamallakin gidan talabijin da rediyo na AIT/Ray Power, su bar ginin da suke ciki cikin awa 48.

A cewar PM News, an shirya rusa ginin da kafar watsa labaran ta ke ayyukanta a ciki a unguwar Ozuoba a Fatakwal, babban birnin jihar, cikin awa 48.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Daga kai kudin fansan a saki matarsa da 'ya'yansa, 'yan bindiga sun rike mai gida

Nyesom Wike
Wike ya umurci masu AIT/RayPower su fice daga ofishinsu cikin awa 48 daga Ribas. Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa Wike ya umurci AIT da Raypower su bar ofishinsu cikin awa 48

An bada wannan gargadin ne cikin wata sanarwar tashi mai dauke da sa hannun sakataren ma'aikatar ayyuka na jihar Ribas, Ebere Dennis Emenike, mai dauke da kwanan wata na 21 da watan Maris.

A cewar sanarwar, cikin na daya cikin wadanda aka zaba don rushe su a unguwar ta GRA Phase 5 a Fatakwal.

Wani sashi na cikin jawabin ya ce:

"Don haka, ana umurtar ku da wannan sanarwar ku kwashe kayan ku cikin awa 48 don bawa masu aiki daman kammalawa cikin gaggawa."

Abin da ke faruwa dangane da Nyesom Wike, AIT, Ray Power, Zaben 2023, PDP, Jihar Ribas

Amma, Kungiyar yan jarida ta Najeriya, NUJ, reshen jihar Ribas, ta roki gwamnatin jihar a madadin kafar watsa labaran cewa ta dakata da shirinta na rushe ginin da kayayyakin AIT/Ray Power ke ciki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Hana FitaDaga Safe Har Dare

Kungiyar ta yi wannan rokon ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban NUJ na jihar, Stanley Job Stanley da Ike Wigodo.

Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike Ya Yi Martani Ga Jawabin Buhari Kan Naira

A wani rahoton da muka kawo a baya kun ji cewa Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya soki haramta amfani da tsaffin N500 da N1000 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a jawabinsa na ranar Alhamis.

Wike ya ce abin da Shugaba Buhari ya aikata kuskure ne saboda hakan ya saba umurnin kotun koli da ta ce a cigaba da amfani da kudin har zuwa lokacin da za ta zartar da hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164