'Yan Ta’addan ISWAP Sun Yiwa Dakarunsu da Sojojin Najeriya Kashe Jana’iza a Cikin Daji

'Yan Ta’addan ISWAP Sun Yiwa Dakarunsu da Sojojin Najeriya Kashe Jana’iza a Cikin Daji

  • ‘Yan ta’addan ISWAP sun yiwa ‘yan uwansu da sojojin Najeriya suka kashe a Borno jana’iza bayan kwanaki kadan da kashe su
  • Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 60 da ‘yan kai a lokacin da suka dakile harin da ISWAP suka kai sansaninsu
  • Ana yawan samun farmakin ‘yan ta’adda, sojoji na yin kokarin lalata mugun nufinsa tare da tabbatar da kai su madakata

Jihar Borno - Bayan sheke da yawan ‘yan ta’addan ISWAP, tsagerun sun taru domin yiwa dakarunsu da sojoji suka hallaka a ranar 19 ga watan Maris a karamar hukumar Mafa ta jihar jana’iza.

Rahotanni a baya sun bayyana yadda sojojin Najeriya suka fatattaki ‘yan ISWAP da yawa, inda suka hallaka wasu tare da jikkata da dama.

Aminiya ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan na ISWAP sun farmaki rundunar sojin Najeriya a dab lokacin da ake tattara sakamakon zaben jihar Borno.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yadda 'yan bindiga suka binne matar sarkn Fulani a Arewa bayan karbar kudin fansa

Rahoto ya shaida cewa, akalla ‘yan ta’adda 60 ne suka rasa rayukansu a lokacin da sojojin suka yi musu kca-kaca, rahoton masanin tsaro a tafkin Chadi; Zagazola Makama.

'Yan ISWAP sun yiwa mamatansu jana'iza a Borno
Jihar Borno mai fama da 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Yan ta’adda sun farmaki cibiyar tattara sakamakon zabe

A cewar rahoto, ‘yan ta’addan sun farmaki cibiyar tattara sakamakon zaben ne da misalin karfe 2 na dare, sa’o’i bayan da gwamna Zulum ya kada kuri’arsa a yankin.

An kwato makamai da mota da sauran kayayyakin aikata laifuka da ‘yan ta’addan suka zo dasu lokacin mummunan farmakin.

A cewar rahoto, ‘yan ta’addan sun fusata, sun ce tabbas za su dauki fansan abin da ya faru na kashe manyan mayakansu, Channels Tv ta ruwaito.

Yanzu dai sun yiwa ‘yan uwansu ‘yan ta’adda jana’iza, ba a san shirinsu na nan gaba ba kan al’umma ko rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Daga kai kudin fansan a saki matarsa da 'ya'yansa, 'yan bindiga sun rike mai gida

Yadda aka sojoji suka kashe ‘yan sanda a Taraba

A wani labarin, kun ji yadda sojoji suka bindige wasu ‘yan sandan da ke bakin aiki a wani yankin jihar Taraba a lokacin zabe.

An ce lamarin ya faru ne a hedkwatar INEC, inda ake tattara sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar a ranar 18 ga watan Maris din da ta gabata.

Ya zuwa yanzu, hukumomin tsaro sun zauna kan lamarin, kuma za su tabbatar da samo bakin zaren don warware duk wata matsala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.