Buhari Ya Yi Alfahari, Ya Bayyana Yadda Ya Hana Siyan Kuri'a A Zaben 2023
- Shugaban kasar Najeriya ya yi alfahari kan yadda gwamnatinsa ta dakile matsalar siyan kuri'a a zaben da aka kammala
- Shugaba Buhari ya tabbatar cewa ya bai wa masu kada kuri'a muhimmiyar shawara kafin zaben
- A cewar shugaban kasar, ya roki ma su zabe da su karbi kudi idan yan siyasa sun ba su amma su zabi abin da ransu ya ke so
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin yadda ya yi iya bakin kokarinsa don tabbatar da ba a siyi kuri'a a zaben 2023 ba.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban yayin da ya ke zantawa da jakadiyar Amurka mai barin gado, Mary Beth Leonard, a fadar gwamnatin kasa a Abuja, ya ce ya fadawa yan Najeriya da su karbi kudin yan takara ma su siyan kuri'a su kuma zabi ra'ayinsu.
Adamawa 2023: A Karshe Gwamna Fintirtiri Ya Magantu Kan Ayyana Zaben a Matsayin Wanda Bai Kammalu ba
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban ya kara da cewa bada damar yin zaben gaskiya da adalci da kuma rashin tsoma baki kamar yadda aka gani a zaben 2023, ya nuna karfin yan Najeriya wajen iya zabar shugabanni.
Da ya ke bayyana gamsuwar shi da yadda yan Najeriya su ka nuna muhimmancin dimokradiyya, zabin da mutane suka yi ya tabbatar da cigaban da aka samu ta fannin dimokradiyya.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana yadda yan Najeriya su ka fara gane karfin su wajen yanke hukuncin wanda zai mulke su a kowanne mataki.
Kalaman Shehu:
''Mutane sun fara fahimtar karfinsu. Bada damar yin zaben gaskiya da adalci, ba wanda zai fada mu su abin da ya dace. Banji dadin faduwar wasu yan takarar ba a zaben.
''Amma na yi farin ciki yadda mutane su ka iya yanke hukunci, sun zabi wanda ya ci sun kayar da wanda ya fadi. Ta hanyar canjin kudi, ba kudin da za a siyi kuri'a, duk da cewa, na ce mutane su karbi kudin su kuma zabi son ran su.''
Buhari ya sabunta nadin shugaban NOSDRA, Idris Musa
A wani rahoton, Shugaba Buhari ya sabunta nadin idris Musa a matsayin shugaban hukumar kiyayye kwararewar man fetur wato NOSDRA.
Ma'aikatar ta Muhalli ta sanar da hakan a ranar Litinin a shafinta na dandalin Twita (@FMEnvng).
Asali: Legit.ng