"Na Kusa Bankwana Da Duniya": Faston Najeriya Yace An Haska Masa Ranar Mutuwarsa, Ya Bayyana Dalili
- Fasto Chukwuemeka Ohaneamere, da aka fi sani da Waliyyi Odumeje, ya yi wani hasashe wanda ya bayyana cewa ya kusa mutuwa
- Dan shekara 40 din wanda ya samar da Mountain of Holy Ghost Intervention and Deliverance Ministry ya ce dalilin zuwan shi duniya ya kammala kuma zai mutu nan ba da jimawa ba
- Waliyyi Odumeje wanda ya bayyana haka ga mabiyansa ya ce ya tattauna da dan shi ya kuma gaya masa ya shirya zama jagoran iyalin shi
Onitsha, Jihar Anambra - A wani abu mai kama da almara, wanda ya kirkiro Cocin Mountain of Holy Ghost Intervention and Deliverance Ministry, Chukwuemeka Ohaneamere, da aka fi sani da Prophet Odumeje ya ce ya kammala aikinsa a duniya kuma zai mutu nan ba da jimawa ba.
A rahoton jaridar Vanguard, sannanen malamin cocin mazaunin Jihar Anambra mai shekaru 40 ya bayyana haka lokacin al'amuran coci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Malamin da ake wa alkunya da Indaboski an ruwaito ya shaida wa mabiyansa cewa lokacin tafiyarsa ya yi.
Na fadawa da na - in ji Odumeje
Odumeje ya ce sun tattauna da babban dan shi, David, ya kuma gaya masa cewa kwanakinsa a duniya sun zo karshe.
Ya fada wa yaron ya shirya zama mai gidan da zai dinga kula da kannensa da mahaifiyarsa idan shi (Odumeje) ya mutu.
Malamin ya bayyana cewa dalilin zuwansa duniya ya kammala
A cewarsa:
''Na kira dan karamin da na, Sarki David, na kuma gaya ma sa kwanan nan, Ni, mahaifinka zan tafi. Dole ka kula da yan uwanka da mahaifiyarka
'' Na zo duniya bisa wani dalili, kuma na cika abin da ya kawo ni. Na kammala aiki na a duniya kuma zan mutu kwanan nan."
Fasto Adeboye Ya Magantu Kan Abin Da Zai Faru Da Duk Wanda Ya Yi Wa Annabi Isa Batanci
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Fasto E.A. Adeboye, babban cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG ya ce duk wanda ya yi batanci ga Annabi Isa (AS) zai gamu da fushin Ubangiji.
Adeboye, ya furta hakan ne yayin da ya ke martani kan yawan hare-hare da aka kai wa coci-coci a sassan Najeriya.
Asali: Legit.ng