Shahararren Mawakin Najeriya, Alhaji Alao, Ya Mutu Yana Da Shekaru 121

Shahararren Mawakin Najeriya, Alhaji Alao, Ya Mutu Yana Da Shekaru 121

  • Allah ya yi wa fitaccen mawaki, Alhaji Jaigbade Aloa, rasuwa yana da shekaru 121 a duniya
  • Hon. Jaigbade, dan marigayin ya sanar da rasuwar mahaifinsa a safiyar ranar Litinin, yana mai cewa an birne shi a gidansa
  • Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazak ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da masoyan mawakin

Ilorin, Kwara - Fitaccen mawaki kuma wanda ke koyar da wakar dadakuada mazaunin Ilorin, Alhaji Jaigbade ya riga mu gidan gaskiya.

Alao, gogaggen mawaki dan asalin garin Ilorin ya rasu a safiyar ranar Litinin yana da shekara 121, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Alhaji Alao
Shahararren Mawakin Najeriya, Alhaji Alao, Ya Mutu Yana Da Shekaru 121. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An birne shi a gidansa da ke Anifowose a Ilorin, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Daga Gama Zaɓe, Gwamnan APC Ya Kori Manyan Hadimansa 2, Ya Maye Gurbinsu

Daya cikin yayan marigayin, Hon. Jaigabade ya bada bayyana rasuwar mawakin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Ilorin.

Sanarwar ta ce:

"Cike da alhini, muna sanar da rasuwar mahaifinmu, kaka, shahararren mawaki dan asalin Ilorin, King (Alhaji) Jaigbade Alao."

Gwamnatin Kwara ta yi ta'azyya ga iyalan Alao

Abdulrahman Abdularazaq, gwamnan jihar Kwara ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mammacin, yana addu'a Allah ya bashi aljanna Firdausi ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Gwamnan cikin sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren watsa labaransa, Rafiu Ajakaye ya ce:

"A madadin gwamnati da mutanen jihar Kwara, ina aika sakon ta'aziya ga iyalan Alhaji Jaigbade Alao da dukkan masoyan wakarsa da Dadakuada a duniya. Alhaji Jaigbade jarumi ne wanda kwarewarsa a irin wakarsa ta haskaka jihar.
"Kuma shugaban al'umma ne. Mutuwarsa ta bar bar gibi a jerin manya da ke tarbiyantar da masu tasowa da ke irin wakarsa ta dadakuada. Muna rokon Allah ya gafarta masa, ya bashi Al-jannah firdaus."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

Mawakin na dadakuada na cikin jaruman da Gwamnatin Jihar Kwara ta karrama a kwanan nan a karon farko da lambar yabo ta rayuwa da aka keɓe ga mutane daban-daban da suka yi aiki ko kuma suka bada gudummawa ga ci gaban jihar ko kasar a matakai daban-daban ko fannoni.

Fafaroma Benedict ya rasu yana da shekaru 95 a duniya

A wani labarin daban kun ji cewa Benedict XVI, tsohon fafaroma na Katolika ya rasu a birnin Vatican.

Ya rasu ne a ranar 31 ga watan Agustan Disamban 2022 kamar yadda jaridar Al-Jazeera ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: