‘Zan Yi Mulki Daidai da Muradin Al’umma’: Abba Gida-Gida Ya Magantu Bayan Lashe Zabe a Kano

‘Zan Yi Mulki Daidai da Muradin Al’umma’: Abba Gida-Gida Ya Magantu Bayan Lashe Zabe a Kano

  • Sabon gwamnan Kano ya bayyana kadan daga abubuwan da ya sanya a gaba a wa'adin mulkinsa
  • Abba Gida-gida ya yi alkawarin tabbatar da samar da ilimi kyauta ga mutanen jihar ta Kano da ke Arewa
  • Hakazalika, ya lissafa bangarorin da zai fi mayar da hankalinsa a wa’adin mulkinsa na shekaru hudu

Jihar Kano - Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi magana mai daukar hankali.

Zababben gwamnan ya yiwa Kanawa alkawarin yin mulki daidai da bukatar al’umma da kuma kawo musu maslaha ga matsalolinsu.

A cewarsa, zai fifita lamarin da ya shafi ci gaban al’umma da kuma samar da ilimi kyauta ga mazauna jihar da ke Arewa maso Yamma.

Abba Gida-gida ya yi alkawarin damawa da Kanawa
Abba Kabir Yusuf, sabon gwamnan Kano | Hoto: The Cable
Asali: Facebook

INEC ta ce Abba Gida-gida ne ya lashe zaben Kano

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: Ganduje ya sassauta, ya dage dokar hana fita da ya sanya a Kano

Idan baku manta ba, rahoton Legit.ng Hausa ya bayyana cewa, INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar Kano, inda ta ce jam’iyyar NNPP ce ta fi yawan kuri’u.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lokacin da ya zanta da kafar yada labarai ta BBC, Abba Gida-gida ya bayyana irin yadda al’ummar Kano ke kaunarsa da kuma karfafa masa gwiwa duk da cewa ya cire rai da sake yin takara.

A cewarsa, bai ji mamakin sanar dashi a matsayin zababben gwamnan Kano ba, saboda ya san irin kaunar da Kanawa ke yi masa.

Kadan daga manufofinsa

A jawabinsa, ya ce zai tabbatar da yaki da cin hanci da rashawa, kuma ba zai yi sako-sako da wannan fannin ba saboda tsiratar da al’ummarsa.

Hakazalika, ya ce zai mayar da hankalinsa ga inganta fannin noma, lafiya, kasuwanci, tsaro da fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Ga fannin ilimi, ya ce zai tabbatar daidaita komai cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa, kuma zai yi ne iyakar kokarinsa.

Abba Gida-gida dai na hannun daman Kwankwaso ne, kuma ya kasance kwamishina a lokacin da Kwankwaso ya yi mulki a shekarun baya.

A dage dokar hana fita a jihar Kano

A wani labarin kuma, kunji yadda gwamnatin Kano ta bayyana dage dokar da ta sanya na hana fita a jihar.

An samu barkewar rikici bayan sanar da sakamakon gwamnan jihar, lamarin da ya kai ga kone gidan mawaki Rarara.

Ya zuwa yanzu, hukumomin jihar sun ce kowa zai iya ci gaba da harkokinsa kamar yadda aka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.