Gwamnatin Kano Ta Ganduje Ta Dage Dokar Hana Fita da Ta Kakaba Wa ’Yan Jihar

Gwamnatin Kano Ta Ganduje Ta Dage Dokar Hana Fita da Ta Kakaba Wa ’Yan Jihar

  • Rahoto ya bayyana cewa, an dage dokar hana fita da aka sanya a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya
  • An sanya dokar ne a baya lokacin da rikici ya barke sadda aka sanar da sakamakon zaben gwamna
  • An samu hargitsi a jihar Kano a zabukan shugaban kasa da na gwamna da aka yi a bana, an yi barna

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta dage dokar ta-baci da ta sanya don tabbatar da bin doka da oda a jihar a lokacin da aka sanar da sakamakon zaben gwamna na jihar.

A jihar, an sanya dokar hana fita biyo bayan sanar da sakamakon zaben gwamna da ‘yan majalisun wakilai na jiha, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan yada labarai na gwamnatin Kano, Muhammad Garba ne ya bayyana dage dokar hana fitan a cikin wata sanarwar da ya ba manema labarai.

Kara karanta wannan

Abba Gida-gida: Sabon gwamnan Kano ya yi magana, ya fadi abin da ya shiryawa Kanawa

Gwamntin Kano ta dage dokar ta baci
Jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar wani yankin sanarwar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Shawarin dage dokar hana fitan ta biyo bayan duba cikin tsanaki ga yanayi da kuma lafawar rikici a fadin jihar.”

Hakazalika, kwamishinan ya yi kira ga bankuna, ma’aikatan gwamnati da sauran jama’ar gari da su fito domin ci gaba da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda aka saba, rahoton Punch.

Yadda rikici ya barke a jihar Kano, an kone gidan Rarara

Idan baku manta ba, an samu hargitsi a jihar Kano bayan da aka sanar da wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar.

Lamarin ya kai ga kone gidan mawakin jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, wanda wasu jama’ar garin ke zargi da yin wakar tunzura jama’a.

Ba sabon abu bane, an yi rikici bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na Najeriya, inda aka sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke a jihar Arewa, an harbe 'yan sanda 2 a hedkwatar INEC

An kama Ado Doguwa bisa zargin hannu a aikin ta’addanci

A wani labarin kuma, kunji yadda aka kama dan majalisar tarayya, Hon. Ado Doguwa na jam’iyyar APC bayan kammala zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.

An zargi Doguwa ne da hannu a ayyukan ta’addancin da suka faru a jihar, musamman a yankin Tudun Wada, inda yake wakilta a majalisar tarayya.

An ruwaito cewa, an kashe wasu mutane tare da kone wasu da ransu a yankin, kuma ana zargin yaransa ne suka aikata hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.