Hukumar Zabe Ta INEC Ta Ce Akwai Kura a Zaben Adamawa, Ta Ce Ya Zama ‘Inconclusive’
- Hukumar zabe a jihar Adamawa ta bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben da aka tattara a jihar
- Ta zargi aringizon kuri'u daga yankunan jihar, inda tace an samu kuskuren da dole a warware kafin ayyana mai nasara
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohi a Najeriya, ba a kawo na Adamawa ba
Jihar Adamawa - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ce akwai kura a sakamakon zaben gwamnan jhar Adamawa, don haka bata amince dashi ba.
Hukumar ta bayyana hakan ne a birnin Yola a cibiyar tattara sakamakon zaben da daren Litinin 20 ga watan Maris.
Ya yi bayanin cewa, an soke zabe a yankuna 47 mai adadin masu kada kuri'u 41,796, wanda ya zarce adadin kuri'u 31,249 da aka kadawa jam'iyyun PDP da APC a zaben na bana.
Hakazalika, an ce Aisha Binani ta jam'iyyar APC ta samu kur'u 390,275 yayin da gwamna mai ci, Ahmadu Finitiri ya samu kuri'u 421,524 a zaben na bana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Cikakken sakamakon da aka sanar
Adadin masu akda kuri'un Adamawa - 2,196,566
Adadin masu akda kuri'un da aka tantance - 859, 964
Sakamakon zabe daga jam'iyyu daban-daban
AA. 641
ADC 2,996
ADP 2,13,4
APC. 390,275
APGA 876
APM. 603
APP 284
LP 2729
NNPP. 4847
NRM 1,237
PDP 421,524
PRP. 1185
SDP. 6,865
YPP. 1,425
ZLP. 199
Sahihan kuri'u 837,820
Kuri'un da suka lalace 14,888
Kadadin kuri'un da aka kada 852,748
An sace masu kai sakamakon zaben jihar Zamfara
A wani labarin kuma, kunji yadda aka sace wasu jami'an hukumar zabe ta INEC da ke kan hanyarsu ta zuwa Gusau daga Maradun don kai sakamakon zaben gwamna.
An ruwaito cewa, ana ci gaba da samun tsaiko ga zaben gwamnan da aka yi a jihar a karshen makon jiya, har yanzu ba a sanar da wanda ya lashe zaben ba.
Sai dai, an ce an sako jami'an, duk da ba a bayyana yadda aka yi suka kubuta ba daga sacesu da aka i ba.
Asali: Legit.ng