Gobara Ta Sake Tashi a Wasu Kasuwanni Biyu a Jihar Kano

Gobara Ta Sake Tashi a Wasu Kasuwanni Biyu a Jihar Kano

  • Wata gobara da ta sake tashi a jihar Kano ta ƙone shaguna da dama a wasu kasuwanni biyu a jihar
  • Gobarar ta tashi ne a wata kasuwar ƴan tumatir a ƙaramar hukumar Bagwai ta jihar da wata kasuwar ƴan waya a ƙaramar hukumar Sumaila
  • A cikin ƴan kwanakin nan gobara na yawan tashi a kasuwannin jihar Kano wacce ke janyo asarar miliyoyin kuɗaɗe

Jihar Kano- Wata gobara da ta tashi ta lalata shaguna 40 a kasuwar tumatir ta Dan Dabino, a ƙaramar hukumar Bagwai ta jihar Kano.

Kakakin hukumar ƴan kwana-kwana ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi shine ya tabbatar da hakan. Rahoton The Guardian

Ganduje
Gobara Ta Sake Tashi a Wasu Kasuwanni Biyu a Jihar Kano Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Kakakin ya bayyana cewa ofishin hukumar na ƙaramar hukumar Bichi ya samu kiran gaggawa daga ofishin ƴan sanda Bichi cewa kasuwar tumatirin Dan Dabino ta kama da wuta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Halaka Basarake da Wasu 2, Sun Sace Mutane Sama da 60 a Jihar Arewa

“Ma'aikatan mu na zuwa kasuwar sai suka ci karo da wani yanki na kasuwar wanda kai faɗin 500 X 300, wanda ake amfani da shi matsayin kasuwar tumatir, yana ci da wuta."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Tawagar jami'an namu sun samu nasarar kashe wutar da hana ta yaɗuwa zuwa wasu shaguna ashirin, wajen taro da wajen ajiye ababen hawa dake kusa da kasuwar tumatirin."

An bayyana cewa dalilin tashin gobarar shine wutar da ake kunnawa ba bisa ƙa'ida ba a kasuwar.

Haka kuma, wata gobarar da ta tashi ta ƙone shaguna bakwai a ƙaramar hukumar Sumaila ta jihar.

Gobarar dai ta tashi ne a dalilin haɗewar wayoyin wutar lantarki a wani shagon siyar da kayan wayoyin hannu.

Gobarar ta ƙona wajen da ake gudanar da harkokin kasuwanci wanda ya kai faɗin 100 X 40.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Ya More Ni Akan Shimfidar Aure, Matar Aure Ta Gayawa Kotu

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin Bagwai mai suna Mallam Bello wanda ya samu zuwa inda gobarar ta auku a kasuwar tumatirin ta Dan Dabino.

Ya tabbatar da cewa gobarar ta laƙume dukkanin rumfunan dake a kasuwar tumatirin waɗanda dama da kara aka yi su.

Ya bayyana cewa gobarar ta janyo asarar dukiyar mai yawa domin babu wani abu da aka samu aka fitar daga kasuwar inda ta cinye komai. Sai dai ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko ɗaya ba a gobarar.

Ganduje ya aike da tallafi

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan ɗari biyu (N200m) ga mutanen da gobarar kasuwannin Singer da Kurmi ya ritsa da su. Rahoton Channels Tv

Gwamnan ya kuma aike da tallafin naira miliyan hamsin (N50m) ga waɗanda gobarar kasuwar Kurmi ta ritsa da su.

A cikin ƴan kwanakin nan an samu tashin gobara a kasuwanni a jihar Kano, wacce ta janyo asarar miliyoyin nairori.

Kara karanta wannan

Kisan Kai: Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Majalisar Tarayya Na Birni a Arewa Ruwa a Jallo, Sun Sa Lada N1m

An Tafka Asarar Dukiyar Miliyoyin Naira Sakamakon Gobara Da Ta Faru A Jigawa

A wani labarin na daban kuma, dukiyar miliyoyin naira ta salwanta a wata gobara da ta tashi a jihar jigawa.

Wutar gobarar ta tashi a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kiyawa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng