Kotun Daukaka Kara Tayi Hukunci Kan Neman Belin Da Abokin Harkallar DCP Abba Kyari Yayi
- Wata kotun ɗaukaka ƙara a birnin tarayya Abuja tayi watsi da ƙarar da abokin harƙalla DCP Abba Kyari ya shigar a gabanta
- Kotun ɗaukaka ƙarar ta ƙi amincewa da buƙatar ACP Sunday Ubua na neman da a bayar da belin sa
- Sunday Ubua yana fuskantar shari'a ne tare da Abba Kyari da wasu ƴan sanda uku na rundunar IRT
Abuja- Kotun Ɗaukaka ƙara tayi watsi da koken da abokin harƙallar dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sanda (DCP), Abba Kyari ya shigar.
ACP Sunday J. Ubua ya shigar da koken ne yana neman kotun da ta bayar da belin sa. Rahoton The Nation
A hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar mai alƙalai uku ta zartar a ranar Juma'a, tace ƙarar tasa bata da tushe.
Mai shari'a Stephen Adah, ya bayyana cewa mai ɗaukaka ƙarar bai kawo wa kotun wasu sababbin abubuwa ba da za su sanya kotun ta sauya hukuncin da mai shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya Abuja, yayi ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai shari'a Adah ya ƙara tabbatar da hukuncin da Nwite yayi a ranar 28 ga watan Maris 2022, inda yayi watsi da roƙon da Sunday Ubua yayi na neman kotun ta bayar da belin sa. Rahoton The Punch
Nwite ya ƙi yarda ya bayar da belin sa saboda masu shigar da ƙara sun gabatar da ƙwararan hujjoji a gaban kotun da suka cancanci hana bayar da belin wanda ake ƙarar.
ACP Ubua yana fuskantar shari'a ne tare da Abba Kyari da wasu ƴan sanda uku na rundunar Intelligence Response Team (IRT), ta hukumar ƴan sandan Najeriya (NPF) kan zarge-zargen safarar miyagun ƙwayoyi da ƙoƙarin ɓatar da hujjoji.
Kotun Koli Ya Tabbatar da Jimkuta a Matsayin Dan Takarar Sanatan APC a Taraba
A wani labarin na daban kuma, kotun ƙoli ta tabbatar da sahihin ɗan takarar sanatan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Taraba.
Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Kaduna, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Zazzafan Umurni
An dai ta samun taƙaddama kan wanene sahihin ɗan takarar jam'iyyar APC a kujerar sanatan Taraba ta Kudu.
Sai dai kotun ƙolin ta tabbatar da sahihin ɗan takarar APC a kujerar sanatan.
Asali: Legit.ng