Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Harin Da 'Yan Ta'adda Suka Kai Jihar Kaduna
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da ƴan ta'adda suka kai kan mutanen da basu ji ba basu gani ba a jihar Kaduna
- Shugaban ƙasar ya kuma umurci jami'an tsaro da su tabbatar cewa sun hukunta waɗannan suka yi wannan mummunan ta'addancin
- Shugaba Buhari ya kuma aike da saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan waɗanda mummunan harin ya ritsa da su
Abuja- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da harin da ƴan ta'adda suka kai a jihar Kaduna wanda ya janyo asarar rayuka da dama.
Shugaban ƙasar ya nuna kaɗuwar sa kan dawowar hare-haren ta'addanci da halaka mutanen da basu ji ba basu bani ba a ƙaramar hukumar Zangon Kataf ta jihar. Rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Shugaba Buhari ya kuma umurci jami'an tsaro da su tabbatar sun gaggauta kamo tare da hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin.
Shugaban ƙasar ya aike da saƙon ta'aziyyar sa ga iyalan waɗanda harin ya ritsa da su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin sa, Garba Shehu ya fitar.
“Akwai wani mummunan hari kan mutanen da basu ji ba basu gani ba a jihar Kaduna, dole ne jami'an tsaro su ɗauki matakin kawo ƙarshen hakan." Inji shi
"Ina miƙa saƙon ta'aziyya ta ga iyalan waɗanda aka halaka a wannan mummunan harin. Allah ya jiƙan su da rahama."
An kai hare-hare a Zangon Kataf
An halaka mutum 10 a harin na Zangon Kataf, wanda ya auku a daren ranar Talata. Sannan kuma wasu mutum huɗu suka samu raunika. Rahoton The Sun
Harin na zuwa ne mako guda bayan ƴan ta'adda sun halaka wasu mutum goma sha bakwai a garin.
Ana Dab Da Zabe, Sarkin Kano Ya Fito Fili Ya Gayawa Mutanen Jihar Abinda Yakamata Su Yi a Zaben Gwamna
Yan Fashin Daji Sun Kashe Manjo, Sojoji 4 da Wasu Jami'an Tsaro a Jihar Neja
A wani labarin na daban kuma, wasu miyagun ƴan fashin daji sun halaka wani babban soja da wasu jami'an tsaro a jihar Neja.
Ƴan ta'addan sun halaka babban sojan mai matsayin Manjo tare da wasu jami'an tsaro a wani tarko da suka ɗana musu.
Asali: Legit.ng