Yan Fashin Daji Sun Kashe Manjo, Sojoji 4 da Wasu Jami'an Tsaro a Jihar Neja

Yan Fashin Daji Sun Kashe Manjo, Sojoji 4 da Wasu Jami'an Tsaro a Jihar Neja

  • 'Yan fashin daji sun yi ajalin Manjo, Sojoji hudu da wasu 'yan banga a sabon harin da suka kai yankuna da dama a jihar Neja
  • Rahoto ya nuna cewa yan ta'addan sun yi wa jami'an tsaron kwantan bauna yayin da suke hanyar zuwa ɗauko gawar wasu da aka kashe
  • Lamarin ya faru da yammacin ranar Talata bayan 'yan bindigan dajin sun aikata ta'asa a kauyukan kananan hukumomi 2 a Neja

Niger - 'Yan bindiga daji sun sake kai sabon kazamin hari yankunan jihar Neja da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, sun kashe jami'an tsaro sama da Takwas.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa yan ta'addan sun kashe mutane akalla 8, cikinsu har da Soja da ya kai matsayin Manjo, wasu sojoji huɗu da 'yan banga.

Sojojin Najeriya.
Yan Fashin Daji Sun Kashe Manjo, Sojoji 4 da Wasu Jami'an Tsaro a Jihar Neja Hoto: vanguard
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun yi nasarar halaka Sojojin da 'yan banga ne yayin da suka ɗana masu tarko a hanyar zuwa ɗauko gawar wasu da aka kashe a yankin Munya

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Majalisa da Aka Sace Ya Gudo, Ya Faɗi Abubuwan da Ya Gani a Sansanin 'Yan Bindiga

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton harin da aka kai kauyukan kananan hukumomin Munya da Paikoro a jihar Neja da yammacin ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindigan, sun yi kwantan bauna a cikin dazuka bayan ɗanyen aikin da suka aikata kan jami'an tsaro ranar Talala, ba zato suka buɗe wa Sojoji da yan sa'kai wuta.

Wani mazaunin kauyen Inu, Inuwa Danladi, ya shaida wa Punch cewa yan ta'addan sun kashe Sojoji huɗu ciki har Manjo da 'yan banga huɗu.

"Yan bindigan mamayar tawagar gamayyar jami'an tsaron suka yi lokacin da zasu wuce da kauyen Sarkin Pawa, suka buɗe musu wuta."

Ya ce tun da safiyar ranar yan bindiga da jami'an tsaron suka yi artabu, daga baya ne 'yan ta'addan suka dawo suka sake farmakan jami'an tsaro.

Danladi ya ce yan bindigan na daji suka birne yan uwansu da suka mutu a musayar wuta, suka samu labarin Sojojin sun taho ɗaukar gawarwakin yan bangan da aka kashe.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Halaka Basarake da Wasu 2, Sun Sace Mutane Sama da 60 a Jihar Arewa

Da aka tuntube shi, kwamshinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya ce an kai hare-hare da dama a jihar kwanan nan amma zai fitar da sanarwa nan gaba.

Dan Takarar LP da Aka Sace Ya Kubuta

A wani labarin kuma Dan Takarar Majalisa da Aka Sace Ya Gudo, Ya Faɗi Abubuwan da Ya Gani a Sansanin 'Yan Bindiga

Ɗan takarar majalisar dokokin jihar Ribas na mazabar Ahoada ta yamma ya shaƙi iskar yanci kwanaki kaɗan bayan wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi.

Da yake jawabi kan abinda ya gani a wurin da maharan suka tsare shi, ɗan siyasan ya ce ba su masa komai ba har zuwa lokacin da suka sake shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262