An Kama Wasu Mutum 7 da Ake Zargin Sun Hallaka Basaraken Gargajiya a Jihar Ebonyi
- ‘Yan sanda sun kama wasu mutum bakwai da ake zargin suna da hannu da kisan wani fitaccen basarake a jihar Ebonyi da ke Kudanci
- An ayyana neman dan takarar gwamnan jam’iyyar APGA a jihar bisa zargin hannu a kisan babban basaraken bayan zaben shugaban kasa
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike kan kisan, kuma wadanda aka kaman suna ci gaba da ba da hadin kai da bayanai
Jihar Ebonyi - Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi sun yi nasarar kame wasu mutum bakwai da ake zargin suna da hannu a kisan basaraken gargajiya, Igboke Ewa na yankin Umuezekoha a karamar hukumar Ezze North ta jihar.
Onome Onovwakpoyeya, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ne ya sanar da batun kama wadanda ake zargin a jihar Laraba 15 ga watan Maris.
TheCable ta ruwaito cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka Ewa ne a cikin gidansa a ranar 26 ga watan Faburairun da ya gabata.
An ayyana dan takarar gwamna a cikin wadanda ake zargi da kisa
Rundunar ‘yan sanda ta ayyana neman Bernard Odoh, dan takarar gwamnan APGA da wasu mutum tara bisa zargin hannu a wannan kisan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, ba a bayyana Odoh daga cikin wadanda ake zargin da aka kama ba a halin yanzu, kamar yadda rahoton NAN ya bayyana.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce, wadanda aka kaman sun hada da Nnabuike Emmanuel, Chukwudi Aliewa, Obinna Nwampepe, Uchenna Eze, Nwogha George, Nnamdi Paul da Odo Kenneth, Punch ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, uku daga cikin wadanda aka kaman sun yi bayanai masu amfani da ka iya kaiwa ga kamo sauran masu hannu a kisan basaraken.
A halin da ake ciki, rundunar na ci gaba da bincike kan tushen lamarin kafin daga bisani a duba dukar matakin da zai kai ga hukunta masu laifin.
‘Yan bindiga sun sace dan takarar majalisar dokokin jiha
A wani labarin kuma, ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani dan takarar majalisar dokoki a jihar Ribas, Chukwudi Ogbonna yayin da zaben gwamnoni ke kara gabatowa.
A halin da ake ciki, ana ci gaba da binciken yadda aka za a ceto dan takarar, ga kuma zaben gwamnoni ya kusa.
Jam’iyyarsa ta Accord ta nemi a daga zaben yankin har sai an tabbatar da ceto dan takararsu kafin a yi zaben.
Asali: Legit.ng