Kwanaki 3 Bayan Rasa Rayyuka 17, Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari

Kwanaki 3 Bayan Rasa Rayyuka 17, Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari

  • Yan ta'adda sun sake kai sabuwar hari a karamar hukumar Zangon Kataf inda suka hallaka mutum 10
  • Hakan na zuwa ne bayan yan kwanaki bayan da yan ta'adda suka kai wani harin a karamar hukumar suka hallaka mutum 17
  • Mr Sam Achie, shugaban kungiyar cigaban Atyap ya tabbatar da harin ya kuma ce sojojin da aka tura garin su tsare su ba su aikin da ya kamata

Kaduna - Yan ta'adda sun sake hallaka mutum 10, ba a ga wasu ba tare da karin mutum hudu da suka yi raunuka a wani sabon hari da suka kai garin Langson da ke karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.

Harin na zuwa ne kasa da kwanaki uku bayan harin Unguwan Wakili da ya jayo asarar rayuka 17 a dai wannan karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Halaka Basarake da Wasu 2, Sun Sace Mutane Sama da 60 a Jihar Arewa

Sojojin Najeriya
Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari A Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: AFP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar cigaban Atyap, Mr Sam Achie, wanda ya tabbatar da faruwar al'amarin ga jaridar Punch, ya ce an gano gawarwaki 10 yayin da ake cigaba da neman sauran.

Akwai sakacin sojoji a kashe-kashen, In ji Shugaban ACDA

Shugaban ACDA ya zargi jami'an sojoji da sakaci a kashe kashen da ake yi a yankin.

A cewarsa, shingen binciken sojoji a yankin baya taimakawa wajen kare su.

Ya yi korafin cewa akwai shingen binciken sojoji kusan guda uku a inda ake kai harin, amma sojojin sun kasa dakile maharan, sai dai sojojin sun hana matasan makwabtan kauyuka da ke son kawo dauki.

A cewarsa:

''Abin takaici har sai da maharan suka gama ta'addancinsu kafin sojoji su kyale matasan''.
''Maganar gaskiya sojoji ba sa kare mu kamar yadda aka kawa su yi. Muna kira ga hukumomin da ya dace da a cire wadannan jami'an sojoji daga garin.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Ki Sakin Ma'aurata Da Diyarsu Bayan Karbar N2m Kudin Fansa, Sun Sake Gabatar Da Wata Bukatar

''Yawan hare hare a yankunana Atyap yunkuri na dakile yankin mutane daga zabar shugabannin da su ke so a zaben Asabar mai zuwa.
''Akwai shirin hana mutane mutanenmu fita zabe ranar Asabar,'' ya fada, ya kuma gara da, ''gwamnati tayi shiru kan irin hare haren da ke faruwa.''

Shugaban ACDA ya jinjinawa yan sanda

Shugaban ACDA na kasa ya yaba da kokarin da kokarin yan sandan kwantar da tarzoma na Langson wanda suka kore maharan, a lokacin da ya ke kira ga al'umma da su cigaba da sanya ido da kare garuruwansu da dukiyoyinsu daga wadanda ke son ganin karshen garin iyaye da kakanninsu.

Mr Francis Sani, ciyaman din Zangon Kataf ya tabbatar da harin

Shugaban karamar hukumar Zango Kataf, Mr Francis Sani, lokacin da ya ke tabbatar da harin, ya bukaci gwamnati da ta kara yawan jami'an tsaro a karamar hukumar don magance faruwar haka da kuma kiyaye rayukan wanda ba su ji ba basu gani ba a yankin.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Jajantawa Yan Kasuwar Kano Da Gobara Ya Shafa

Jaridar Punch ta ruwaito cewa maharan sun mamaye yankin da misalin 9:00 na daren Talata, suna harbi kan mai uwa da wabi, tare da fasa shaguna kafin yan sandan kwantar da tarzoma su kora su.

Yan bindiga sun halaka limami sun sace mutane 14 a Kaduna

A wani harin duk dai a Kaduna, kun ji cewa yan bindiga sun yi awon gaba da limamin masallacin Juma'a a Rugan Ardo, Isyaka Adamu da wasu mutane a karamar hukumar Kagarko.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, wani mazaunin garin, Shehu Ibrahim ya tabbatar da afkuwar harin a hirar wayar tarho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164