Hotunan Dan Inyamuri Mai Siyar da Tsire Ya Ba da Mamaki, Jama’a Sun Yi Martani
- Wani matashi dan kabilar Inyamurai da ke sana’ar fawa ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta cikin kwanakin nan
- Sana’arsa ta fawa ta bayyana ne a kafar sada zumunta ta Facebook bayan da cikin alfahari ya tallata hakan a kafar
- Jama’ar kafar sada zumunta sun yaba masa, sun kuma yi mamakin yadda ya tsara tare da kimtsa komai cikin tsanaki
A shekarun baya, ‘yan Najeriya da dama suna da ra’ayin cewa, siyar da tsire, kilishi da balangu sana’a ce da ta zama kebabba ga al’ummar Arewa.
A wannan karon, lamarin ya zo da sabon salo yayin da wani matashi Felix Aden ya fito da salon siyar da tsire duk da yana Inyamuri.
Felix, matashin dan kabilar Inyamurai ya sauya tunanin jama’a, inda ya bayyana sana’arsa mai alaka da Hausawa a kafar sada zumunta.
Matashin ya yada yadda yake sana’arsa a shafin Facebook na Popular Nigerian Dishes, inda ya bar jama’ar kafar baki bude.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A daya daga hotunan da ya yada, an ganshi sanye da rigar fawa da hula, a wani hoton kuma, an ga lokacin da ya jera tsinkayen tsiren da yake siyarwa.
Martanin jama’a a Facebook
Jama’ar kafar sada zumunta ta Facebook sun yi martani mai daukar hankali game da sabuwar sana’arsa ta fawa.
Zwelin Ebubedike Elvis:
"Kun gani, ku duba yanzu.
“Ya sha tsari da tsafta sosai.
‘Wannan shine bambancin kasuwancin Inyamuri da Bahaushe.”
Tunde Siwoku:
"Kai ya yi masa kyau! Ba sa bukatar Bahaushe a Anambra don siya da tsire yanzu.”
Franklin Ugonna Oparaji:
"Komai a tsaftace, matashin ya yi kyau kuma ga tsafta.
“Araha bata ado, ado ba sa’an araha bane. Muje zuwa!!!”
Pretty Ella:
"Kai! Kasuwarsa za ta karbu saboda shine Inyamuri na farko da ya fara hakan kuma tabbas zai zo da bambanci.”
Hakeemah Abdullahi:
"Don Allah ka zama saurayina kuma tsinken tsire nawa za ka ke bani a kullum ina son sani.”
Angela Francis:
"Na san wannan, yana nan a titin Ezeiweka Awada Obosi kusa da magamar Ukaegbu.”
Abela Olayemi Salami:
"Gaskiya akwai tsafta da kyan gani a fuska...amma akwai matsala, zan ji tsoron cinsa saboda wasu dalilai.”
Asali: Legit.ng