Kwankwaso: Yadda Na Hango Hadari, Na Yi Wa Buhari Alherin da Ya Ceci Rayuwarsa
- Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a kan kyautar motar da ya taba Muhammadu Buhari
- A lokacin yana Gwamna, Kwankwaso ya fahimci rayuwar Buhari ta na cikin hadari a Najeriya
- Wannan ya sa ‘Dan siyasar ya bada mota domin kare tsohon sojan, a karshe motar ta ceci rayuwarsa
Kano - A wata zantawa da yake yi da jama’a kwanan nan, an ji Rabiu Musa Kwankwaso yana gargadin cewa ana fuskantar barazana a halin yanzu.
Kamar yadda wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi ya nuna, wannan magana ce ta jawo Rabiu Musa Kwankwaso ya dakko wani tsohon labari.
‘Dan siyasar ya ce za a iya cewa kwakwalwarsa ta musamman ce, har Muhammadu Buhari zai shaida haka saboda zurfin tunaninsa ya yi masa rana.
Kwankwaso yake cewa a shekarun baya ya taba lura za a iya kawowa Buhari hari, saboda haka ya tanadan masa mota wanda harsashi ba zai ratsa ta ba.
Mota ta ceci Buhari a 2014
Jim kadan bayan ya samu wannan mota sai aka kai wa tsohon shugaban kasar (a lokacin) hari, kusan a sanadiyyar motar da aka ba shi kyauta ya yi rai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dr. Abdulaziz Tijjani Bako ya daura wannan faifai a shafinsa, a nan aka ji tsohon Gwamnan yana cewa rikici zai barke da an taba Janar Buhari a 2014.
"Tun da na kwankwasa gilashin motarsa, na ce a wannan Buhari yana cikin hadari. Na ce a bincika mani a gani ko yana da ‘bullet proof’, aka ce bai da ita.
Cikin mako biyu na sa aka shigo da ‘bullet proof’ dinnan, aka zo yana cikin wannan mota Na san ana shirin kai masa hari, kuma na san idan aka same shi, ba kashe shi ne matsalar ba
Fitina za ta tashi a kasar nan, a ce gwamnati ce a wannan lokaci ta shirya, kowa ba zai yarda ba a Arewa."
- Rabiu Kwankwaso
An gamu da hadari a Kaduna
"Mu ka saya, aka je aka yi hadari, ya bugo mani waya ya ce duk wadanda ke kewaye da su sun mutu, su kadai ne da ke wannan mota ba su mutu ba.
Abin da ya sa nake fada saboda ya riga ya fito da maganar ne, ya ce da ni mai kyauta ne."
- Rabiu Kwankwaso
Tsohon Ministan tsaron ya ce kamata ya yi Shugaba Buhari ya ce Sanata Kwankwaso akwai tunani, domin shawarar da ya kawo ta fi karfin dukiya.
Kwankwaso wanda ya nemi takarar shugaban kasa a NNPP a 2023, ya ce ba kudin motar ce abin dubawa ba, ko iyaka shawarar ya kawo, ya ceci al’umma.
Kutse miliyan 13
A wani rahoto, an ji Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce yunkurin yin kutse a shafukan yanar gizon Najeriya ya kusa dosar miliyan 13 a lokacin zabe.
Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce kafin zabe ana fama da harin kutse 1,550,000 a kowace rana, adadin kutsen ya karu da miliyan 6 da ake zaben shugaban kasa.
Asali: Legit.ng